Rahotanni daga jihar Sakkwato, sun bayyana cewa wani Kwalekwale ɗauke da fasinjoji kusan arba’in ya kife a kogin Dundaye, da ke ƙaramar hukumar Wamakko ta jihar.
Akasarin waɗanda lamarin ya rutsa da su dai mata ne da ƙananan yara yayin da suke ƙoƙarin haye kogin akan hanyarsu ta zuwa gonakinsu.
- An Yi Garkuwa Da Sarkin Gobir Da Wasu Mutane 5 A Sokoto
- Jam’iyyar PDP Ta Janye Daga Shiga Zaɓen Ƙananan Hukumomi A Kebbi
Wani shaidar gani da ido ya tabbatar da cewa masu ninkaya a ƙauyen sun ceto kimanin mutane goma sha biyar, inda kimanin ashirin da biyar suka ɓace yayin da ake ci gaba da bincike.
Mashawarcin gwamnan Sokoto, na musamman kan hukumar bayar da agajin gaggawa, Nasir Garba Kalambaina, ya ce tuni tawagar masu aikin ceto da kuma jami’an hukumar bayar da agajin gaggawa ta ƙasa sun isa zuwa ƙauyen don gudanar da aikin ceto.
An dai alaƙanta wannan haɗarin ne da malalar kogin Dundaye, da ke ƙaramar hukumar Wamakko a jihar.