Kwalliya wata aba ce da take kara fidda kyawun ‘ya mace musamman ga wanda ya iya tsara ta, akan sami akasi ga wanda bai iya yin ta ba, ta hakan ne ake kallon wasu ko da sun yi kwalliyar ba za a ga kyan kwalliyar su ba.
Kwalliya ta rabu kashi daban-daban kamar yadda su ma kayan kwalliyar nau’ikansu suka rabu daban-daban. A yanzu kwalliyar fuska ta canja salo da tsari irin na burgewa daga lokutan baya zuwa lokutan yanzu, wanda su ma kansu kayan kwalliyar suka canza fiye da lokutan baya.
- Ana Ci Gaba Da Nuna Damuwa Kan Watsi Da Aikin Tashar Baro
- Sin Ba Ta Amince Da Mu’amalar Gwamnati Tsakanin Yankin Taiwan Da Amurka Ba
A yanzu kwalliya na taka rawar gani wajen taimakawa matasa samun aikin yi ta yadda ta zama babbar sana’a ga wanda ya iya tsara ta.
A kowanne lokaci mata na zama su tsara kwalliyarsu ko kuma su je a yi musu musamman a lokutan shagulgulansu kamar daga bikin aure, suna, shagalin Sallah, karin shekaru, da dai sauransu, lokaci zuwa lokaci kwalliya takan canja daga tsarin da aka san ta zuwa wani nau’in tsarin daban.
Ko wanne tanadi mata su ka yiwa kansu wajen inganta kwalliyar fuska a wannan lokaci ko na ce a wannan zamanin? Ko ma dai mene ma gani.
Akwai nau’ika da dama na kayan kwalliya kuma kowanne yana da nasa fa’idar na musamman kamar ‘Foundation’ a kan yi amfani da ita a fuska tare da zabin nau’in kalar fatar mutum, akwai su ‘Lipsticks’ shi ma yana da nau’ika daban-daban na ruwa da wanda ba na ruwa ba, da masu haske da marasa haske, me kyalli da mara kyalli, yakan taimaka wa labba wajen ganin sun yi laushi da kuma canja launi da kyalli.
Kayan da ake amfani da su wajen yin kwalliya na da yawa akwai ‘Brush’, ‘Bronzer’, ‘Toner’, ‘Tanning Lotion’, ‘Brightener’, ‘Nail Polish’, ailana, Maskara, firaima, kwansela, fes kirim, mostiraiza, Miro, lif laina, aishado, kilinza, lif sitik, da dai sauransu.
Kawai ki shirya tsara kwalliyarki da wadannan kayan kwalliya da na lissafa da ma wasu da kuke jin dadinsu da ban kawo ba wajen birge maigida ko kuma fitar da kyawun da Allah ya yi miki rangadadas!