Hukumar kwallon kafa ta duniya (FIFA), ta mayar da wasan zagayen karshe na neman shiga cin kofin duniya na mata ‘yan kasa da shekaru 20 na shekarar 2024, tsakanin Nijeriya da Burundi daga Bujumbura ta kasar Burundi zuwa Dar es Salaam da ke makwabciyar kasar Tanzania.
FIFA ta yanke shawarar daukar wannan matakin ne domin abin da ta kira rashin kyawun filin wasan da tun farko aka shirya za a buga wasan, inda ta ce bai dace da karbar bakuncin wasan ba.
- Emefiele Ya Musanta Zargin Bude Asusun Banki 593 A Kasashen WajeÂ
- Gwamnatin Sakkwato da Wamakko Sun Tallafa Wa Mutane 66 Da Sojoji Suka Ceto
Tsakanin Nijeriya da Burundi duk wadda ta yi nasara za ta samu tikitin zuwa kasar Colombia inda za a buga kofin duniya na mata ‘yan kasa da shekaru 20 a 2024.
Yanzu dai Burundi za ta karbi bakuncin Falconets a filin wasa na Azam da ke birnin Dar es Salaam, inda ‘yan Nijeriya suka tashi kunnen doki 1-1 da takwarorinsu na Tanzania a zagayen da ya gabata kafin daga bisani suka doke su da ci 2-1 a Abuja, abin da ya kawo su wannan mataki.