Tawagar mata ta Super Falcons ta Nijeriya na dab da samun gurbin shiga gasar cin kofin Afrika ta mata na 2024 bayan ta doke Cape Verde da ci 5-0 a Abuja.
Zakarun Afirka sau tara, Super Falcons, sun taka rawar gani duk da cewa sun rasa wasu manyan ‘yan wasa da suka hada da Asisat Oshoala, Michelle Alozie, Christy Ucheibe, da Ifeoma Onumonu.
- Super Falcons Sun Dawo Gida Bayan Fitar Da Su Daga Gasar Kofin Duniya
- NNPP Ta Nemi EU, Amurka Da AU Su Kawo Mata Dauki Kan Zaben Gwamnan Kano
Masu masaukin baki ba su dauki lokaci mai yawa ba kafin su zura kwallaye a ragar Cape Verde, inda Uchenna Kanu ta zura kwallo bayan mintuna bakwai kacal da fara wasan.
Mai tsaron raga Chiamaka Nnadozie tayi kokarin hana kwallo shiga a wani bugun daga kai sai mai tsaron raga da Cape Verde ta buga.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp