Kwamishinan Sufuri na Jihar Kano, Alhaji Ibrahim Ali Namadi Dala, ya yi murabus daga mukaminsa sa’o’i kaɗan bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya karɓi rahoton kwamitin binciken da ake a kansa karɓar belin wani da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi, Sulaiman Aminu Danwawu.
Mai magana da yawun gwamnann Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ne ya fitar da sanarwar ajiye muƙamin Kwamishina Namadi, ya kuma bayyana cewa Namadin ya yanke shawarar yin murabus ne saboda mahimmancin ɗaukar matakin da samar da masalaha.
- Kwamitin Bincike Ya Miƙa Rahoto Kan Kwamishinan Sufuri Ga Gwamnatin Kano
- Yadda Kwamishinan Kano Ya Karɓi Dala $30,000 Domin Yin Belin Dilan Ƙwaya A Kotu – Rahoto
“Kasancewa ta a cikin gwamnatin da ke fafutukar yaƙi da sha da sayar da miyagun ƙwayoyi, ya zama dole in ɗauki wannan matakin, ko da kuwa zai zama ba me sauƙi ba a gare ni,” Cewar Namadi.
Alhaji Namadi ya gode da damar da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ba shi na yin wa jihar hidima, yana kuma sake jaddada biyayyarsa ga shugabanci da jagorancin gwamna Abba Yusuf.
Tuni, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya karɓi ajiye muƙamin tare da yi wa tsohon kwamishinan fatan alheri a sauran harkokin rayuwarsa ta gaba.
Gwamnan ya kuma jaddada kudirinsa na ci gaba da tabbatar da adalci, ladabtarwa, da yakar laifukan da suka shafi sha da fataucin miyagun kwayoyi da sauran munanan dabi’u da ke addabar matasa da al’umma jihar Kano.
Gwamna ya kuma yi gargaɗi ga duk masu rike da mukaman siyasa da su rika yin taka-tsantsan kan al’amuran da suka shafi jama’a, tare da neman izini daga hukuma kafin su shiga irin waɗannan harkoki marasa daɗi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp