An gudanar da cikakken zama karo na biyu, na kwamitin ladabtarwa da sanya ido na kwamitin kolin JKS karo na 20, daga ranar 9 zuwa 10 ga wata, inda aka tsara dabaru kan daukar kwararan matakan tafiyar da harkokin jam’iyya bisa tsauraran matakan da’a. Taron ya jaddada zurfin ci gaban salon jam’iyya, da tsaftatacciyar gwamnati, da yaki da cin hanci da rashawa, kana da zurfafa ci gaba mai inganci na ayyukan duban ladabtarwa da na sa ido a cikin sabon zamani, da sabon tafarki, ta yadda za a bayar da garanti mai karfi na kafa wani mafari mai kyau, na gina kasar Sin mai salon gurguzu ta zamani.
Kwamitin kula da ladabtarwa da sa ido, na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, shi ne hukumar bincike da sa ido na kwamitin kolin JKS. Muhimman ayyukansa su ne kiyaye kundin jam’iyyar da sauran ka’idojinta, da duba hanyoyi, da ka’idoji, da manufofi na jam’iyyar, da kuma yadda ake aiwatar da kudurori, kana da taimakawa kwamitin jam’iyyar wajen karfafa salon jam’iyya, da tsarawa, da daidaita ayyukan yaki da cin hanci da rashawa. (Mai fassara: Bilkisu Xin)