Yau Jumma’a, ofishin siyasa na kwamitin tsakiyar Jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin (JKS) ya kira taro, domin tantance yanayin da tattalin arzikin kasar ke ciki, da ayyuka masu nasaba da tattalin arziki. Inda babban sakataren kwamitin tsakiyar JKS, Xi Jinping, ya jagoranci taron.
A yayin taron, an bayyana cewa, ya kamata a aiwatar da sabbin ra’ayoyin neman bunkasuwa bisa dukkan fannoni, tare da gaggauta aikin gina sabon tsarin neman ci gaba, da kuma neman daidaito a tsakanin aikin raya tattalin arzikin kasa da yakin ciniki na duniya. Kana, ya kamata a mai da hankali wajen samar da isassun guraben aikin yi ga al’umma, da tabbatar da zaman karko na kamfanoni da kasuwanni cikin gida, tare da kiyaye hasashe mai yakini da ake yi kan bunkasuwar tattalin arziki, domin tinkarar kalubaloli ta hanyar samun ci gaba mai inganci.
A taron har ila yau, an kuma jaddada cewa, ya dace a yi amfani da manufar raya sha’anin hada-hadar kudi, da manufar samar da karin kudade a kasuwa yadda ya kamata. Da kuma ba da taimako ga jama’ar dake samun matsakaicin kudin shiga da kananan kudin shiga, don su samu karin kudaden shiga, tare da kuma kara kudaden da za a kashe kan harkokin hidima, ta yadda za a inganta bunkasuwar tattalin arziki. Haka zalika kuma, ya kamata a ba da taimako ga kamfanonin dake fama da matsaloli ta hanyoyi daban daban, tare da warware matsalolin da ake fama da su a lokacin neman ci gaba, ta hanyar zurfafa aikin yin kwaskwarima da bude kofa ga kasashen waje. (Mai Fassara: Maryam Yang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp