Gwamnatin Jihar Kaduna ta ayyana kungiyar da ke rajin bunkasa al’ummar Atyap (ACDA) a matsayin haramtacciyar al’umma a jihar kuma ya tabbata hannu kan dokar haramta ta.
A sanarwar manema labarai da Kakakinsa, Muyiwa Adekeye, ya fitar a ranar Lahadi, ya ce, kungiyar da aka haramta ta kafa kanta a matsayin kungiyar bunkasa al’ummar Atyap da ta kafa kanta a cikin al’ummar da ke cin gajiyar zaman lafiya kuma take gudanar da ayyukanta a sirrince, “Ta shiga aikin da ke barazana ga zaman lafiyan da kwanciyar hankali da kyakkyawar shugabancin da ake da shi a jihar Kaduna.”
Sanarwar ta ce gwamnan da ke shirin barin gado, Malam Nasir El-Rufai, ya sanya hannu kan dokar haramta ‘Atyap Community Development Association’ ne bisa dogara da sashin doka na 60 na kundin final kod ta Jihar Kaduna mai lamba 5 ta shekarar 2017 da kuma sashi 5 (2) ba kundun tsarin mulkin kasa
“Haramcin ta fara aiki ne daga ranar 24 ga watan Mayun 2023,” ya kara da fada.
Adekeye ya ce dokar haramtawa ta yi nuni da cewa sashe na 38 da na 40 na kundin tsarin mulkin tarayyar Nijeriya sun tabbatar da ‘yancin fadin albarkacin baki, da yin addini yadda mutum ya fahimta da kuma ‘yancin yin kungiya ko yin taro a bainar jama’a cikin lumana ga dukkan ‘yan kasa.
Sanarwar ta kara da cewa: “Har ila yau, an lura cewa sashe na 45 (1) na kundin tsarin mulkin kasa na 1999 ya bai wa Gwamna ikon daukar irin wadannan matakai da ayyukan da suka wajaba don ingantawa da kare lafiyar jama’a, zaman lafiyar jama’a, tarbiyyar jama’a ko lafiyar jama’a ko ’yancin kowa da kowa a Jihar Kaduna.”
Don haka ne ya ce bisa lura da take-taken kungiyar na kawo cikas ga zaman lafiyan jihar ne ya sanya suka haramtata.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp