Kwanaki biyu bayan kashe wasu masunta 20 a kauyen Gadan Gari da ke karamar hukumar Bama a jihar Borno a ranar Laraba, ’yan ta’addar Boko Haram/SWAP sun kashe wani Kwamandan Sojoji da wasu manyan jami’an soji biyu da sojoji 17 a wani sansanin soji da ke garin Malam Fatori, karamar hukumar Abadam da ke jihar.
Bama tana tsakiyar Borno ne yayin da Malam Fatori ke karamar hukumar Abadam a arewacin jihar, tsakanin jihar Borno da Jamhuriyar Nijar.
- Yadda ‘Yan Bindiga Suka Yi Garkuwa Da Mutane 22 A Ƙauyuka Biyu A Kaduna
- Mutane Da Dama Sun Rasu Sakamakon Bindigar Tankar Mai A Enugu
A harin na baya-bayan nan, majiya mai tushe ta ce, a ranar Juma’a, 24 ga watan Janairu, 2025, ‘yan ta’addan sun kai hari kan bataliya ta 149 da ke Malam Fatori inda suka tarwatsa sansaninsu.
Majiyoyin leken asirin da suka tabbatar da harin, sun kara da cewa maharan sun kai hari sansanin ne dauke da muggan makamai, inda suka ce ‘yan ta’addan sun lalata gine-gine da dama da kuma motocin aikin soji a yayin harin.