A cikin bukukuwan zagayowar ranar haihuwar tsohon gwamnan Jihar Kano, Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso na shekaru 67 da haihuwa, Kwankwaso ya kaddamar da cibiyar nazarin harkokin karatun alkur’ani da ya rada wa sunan mahifinsa, Marigayi Majidadi.
Da yake gabatar da jawabinsa a lokacin taron, Kwankwaso ya ce, “Muna gode wa Allah, tun mana raye irin abin alkairin da muka shuka lokacin da muke mulki Jihar Kano mun fara ganin alfanunsa.
“Muna shawartar duk wani mai kishin ci gaban al’umma da ya ci gaba da samar da iren-iren wadannan makarantu, musamman ganin irin alfanunsu ga rayuwar ‘ya’yanmu. A lokacin da muke mulkin mun samar da makarantun nazarin ilimin addini a daukacin kananan hukumomin Jihar Kano 44, wanda bayan tafiyar mu aka yi watsi da su,” in ji shi.
Ya ce an tsara wannan cibiya ne domin daukar yara mahaddata alkur’ani masu shekaru 15 zuwa 25, saboda ba su cikakken horo tare da samun kyakkyawan yanayin gudanar da harkokin karatun alkur’ani.