Wani kwararre ‘dan kasar Birtaniya ya bayyana cewa, a lokacin da ake tsara sabbin manufofin tattalin arziki, da tsara turbar zamanantar da kasar, gwamnatin kasar Sin tana sauraron abin da al’ummarta ke bukata, ta kuma yi aiki a kai.
A wata hira da kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya yi da shi a baya-bayan nan, Stephen Perry, shugaban kungiyar da ake kira “Britain’s 48 Group Club” ya bayyana cewa, burin kasar Sin na samar da ayyukan yi kimanin miliyan 12 a biranen kasar a shekarar 2023 da aka tsara a cikin rahoton ayyukan gwamnati na bana ya burge shi matuka.
Perry, ya ce, abin da yake bunkasa tattalin arzikin kasar Sin, shi ne bukatar samar da ayyukan yi ga matasan da ke kammala karatu daga jami’o’i da dai sauransu.
Ya kara da cewa, hakan na nufin kasar Sin ta mai da hankali ba kawai kan abin da zai taimaka ga ci gaban GDP na wannan shekara ba, ba kawai daga wane bangare za ta fito ba, a’a, mene ne babban batu a cikinta, kuma shi ne ci gaba da samar da aikin yi da kuma bunkasar kasar. (Mai fassarawa: Ibrahim)