Manyan jami’ai da kwararrun nahiyar Afirka, sun jinjinawa saurin zurfafar hadin gwiwa tsakanin kasashen Afirka da Sin a fannonin kimiyya, da fasaha, da kirkire-kirkire, suna masu bayyana hakan a matsayin ginshikin haifar da managarcin sauyi a kawancen sassan biyu, wanda ke da matukar muhimmanci ga cimma nasarar zamanantarwa, da wanzar da ci gaba a dukkanin sassan Afirka.
Sun bayyana hakan ne a ranar Juma’a, yayin taron ranar hadin gwiwar kirkire-kirkire ta Sin da Afirka, wadda aka gudanar a helkwatar kungiyar tarayyar Afirka ta AU, dake birnin Addis Ababa, fadar mulkin kasar Habasha, karkashin taken “Sabbin damammaki domin hadin gwiwar kirkire-kirkire: Hada hannu don cimma nasarar zamanantarwa.”
Da yake tsokaci game da batun, ministan ma’aikatar kirkire-kirkire da fasahohi na kasar Habasha Belete Molla, ya bayyana muhimmancin hadin kai a matsayin jigon dunkulewar kasashe masu tasowa da masu saurin bunkasa, wanda ke sauya fasalin makoma, da yanayin ci gaban duniya baki daya. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp