Nada sabon Shugaban Babban Bankin Nijeriya, Dakta Michael Olayemi Cardoso, zai taimaka wajen samar da kwanciyar hankali da daidaito a tsarin gudanar da babban bankin da irin ci gaban da ake bukata a halin yanzu don farfado da tattalin arzkin kasa.
Wannan kuma, kamar yadda masana da dama suke bayani tare da fashi bakin yadda nadin zai taimaka wajen warware manyan matsalolin da bangaren tattalin arzikin kasar nan ke fuskanta musamman wadanda suke cutar da al’umma kasa.
- Za Mu Tabbatar An Hukunta Masu Zaluntar Kananan Yara Da Mata – Kwamishina Rabi Salisu
- Matsayin Kasar Sin Na Adawa Da Matakin Japan Na Zuba Dagwalon Nukiliya A Cikin Teku Bai Sauya Ba
Wannan kuma yana zuwa n a daidai lokacin da shugaban kasa, a masatyinsa na kwararre ke yin abin da ya dace don tabbatar da tattalin arzikin kasa yana tafiya yadda ya kamata.
Kafin nada shi, Cardoso, wanda ma’aikacin banki ne kuma kwararren mai shirya harkokin al’umma, ya yi aiki a masatyin kwamishinan tattalihn arziki da tsare-tsaren kasafin kudi a karkashin Gwamna Tinubu a Jihar Legas. Duba da wannan ana iya cewa, kwararre ne a kuma yana da sanin makamin aiki na tafiyar da Babban Bankin Nijeriya, a matsayin wata cibiyar gwamnatin tarayya da ke da karfi a wajen gudanar da tsare-tasren kanana da matsakaitan masana’antu har ma da manyan masana’anatun kasar nan da abin da ya shafe su gaba daya. Wasu kuma na ganin wadannan kwarewa ba za su yi wani tasiri mai yawa ba in aka lura da cewa, wani tsohon shugaban Babban Bankin Marigayi Alhaji Adamu Ciroma, ya karanta Tarihi ne a jami’a amma da marigayi shgugaban kasa Janar Murtala Mohammed ya nada shi ya yi aiki yadda ya kamata kuma ya ba mara da kunya, daga baya kuma aka nada shi a masatyin Ministan kudi saboda cancantarsa.
Amama dai koba komai yana ya hau karagar shugabancin ne a daidai lokacin da al’umma ke zura ido su ga irin tasirin da zai haifar musamman ganin yadda ake fuskantar mastalar hauhawar farashi, karyewar darajar Naira, da raguwar tasirin naira a kan kudaden kasashen duniya da kuma mastaloli da dama da suka yi wa tattalin arzikin kasa katutu.
Adaidai wannan lokacin ne, mai sharhi zai tsaya ya yi Nazari don fahimtar cewa, Cardoso, wwanda ya yi karatun digiri a fannin gudanarwa a jami’ar Aston da ke Birtaniya ya kuma yi karatun babban digiri na biyu a jami’ar H Harbard ta kasar Amurka, tabbas wanann aiki ya yi daidai da shi.
‘Yan Nijeriya na masa fatan fara aiki nan take babu gudu babu ja da baya wajen samar da tsare-tsaren da za su dawo da tattalin arzikin kasa hayyacinsa. Mutum zai samu kwarin gwiwa in aka lura da cewa yana a kan akidar shugaban kasa Asiwaju Tinubu kamar yadda ministan kudi Wale Edun, yake shima daga akidar Tinubun ya fito dukkan su za su taimaka wa juna wajen tabbatar da nasarar tattalin arzikin kasa, tare da samar da tsare-tsaren da za su taimaki shirin shugaban kasa na fitar da kasa daga kangin matsalolin tattalin arziki da suka yi wa Nijeriya katutu tun mulkin gwamnatiocin a suka shude.
Wannan al’amarin daukar mataki akan shi ya zama dole bama kamar yadda ake ma shi ganin shi na hannun daman Shugaban kasa Tinubu ne don haka wasu ke ganin yana danyan ganye da shi.
Koda kuwa hakan gaskiya ne idan aka yi la’akari da irin siyasar Nijeriya wadda ta sha bamban da irin ta Legas, akwai abubuwan da sai an yi amfani da su musamman ma idan aka yi la’akari da yin adalci kan al’amarin da ya shafi sashe ko bangaranci. akan ayyukansa a matsayinsa na gwamnan Babban Bankin kasa.
Wato dangane da yadda yake hulda da Shugaban kasa da kuma Ministan kudi, ya dai dace a tunatar da shi ya dace ya daidaita yadda mizanin tafiyar tattalin arziki yakamata ya kasance, saboda al’amarin ya zama tamkar wata zumangiyar kan hanya ce da take bugun yaro da babba.
Wannan al’amari ko shakka babu ba karamin taimakawa yake ba wajen yadda tattalin arziki ya shafi rayuwa yake shafar rayuwar fiye da tsammanin kowa, irin haka kuma ba za asaba da shi zai yi kuma a samincewa da al’amarin.
Ba sai ya tsaya an fada ma shi irin yadda al’umma suke matukar fuskantar wahala wajen tafiyar da rayuwarsu ta yau da kullun, ba domin komai ba sai saboda yadda ake ta fuskantar matsaloli masu yawa wadanda ragon tattalin da ke fuskanta cutar da ke da wuyar magani.
A matsayin sa na wanda yake da wuka da nama na bangaren tattalin arziki sanin kowa ne shi ne mai ba Shugaban kasa shawara ta fannin tattalin arziki, kowa na san ran zai yi tunanin da zai taimaka wajen samar da hanya mafita ba ma sai ta fannin daya fi sani ba na tattalin arziki.Yana iya bullowa ta tsare- tsaren da za su taimakawa al’umma ba sai sun ji a jikinsu ba.Akwai ma al’amarin iya mu’amala da mutane hakan ma zai taimaka idan kuma ba ayi hakan ba, ba wani abin mamaki bane idan har an hadu da wani cikas ko matsala akan hanya.
Wani abinda ake ganin ya yi kaka-gida ko samarda katsalandan ba wani abu bane illa yadda aka dogara da shigo da kaya daga waje da kuma al’amarin siyasa yadda aka shigar da shi a abinda ya shafi kudaden kasashen waje nan ma dai sa idon na jada abubuwa su koma baya.
Idan har hakan ya zama gaskiyar halin da ake ciki dole ne mukamin da aka bashi ya tsone idanun wasu, ba kuma wani abin mamaki bane aga wasu ko gane ba aji dadi ba kan mukamin da aka bashi saboda wasu bukatun da ake daga wurinsa ba dole ba ne a same su cikin kankanen lokaci ba.
Duk da haka dai ‘yan Nijeriya suan sa ran sai ya sa kafar wando daya da wasu har ma da wadanda ake yi ma kallon sun fi karfin ayi masu hakan, muddin dai har ana son wajen lura da kudaden da sike asusun Nijeriya da yake waje, sanin kowa ne dai al’amarin yana tangal- tangal, sanin kowa ne irin asusun ajiya dake waje shi ne yake taimakawa yawancin al’umma, kamar dai yadda idan aka yi ma al’amarin rikon sakainar kashi ‘yan kalilan ne za su yi facakar da zata sa al’umma cizon yatsa a haba.
Hakanan ma kafa ayi tsammanin wanda zai haua kujerar gwamann Babban Bankin kasa zai daga sau Banki ya ci gaba da zama mai tafiyar da harkokinsa, hakan kuma zai sa a kauce ma tunkarar akama wasu hanyoyin da za su sa ayi dana-sani akan wasu matakan da ba za su iya taimakawa ci gaban tattalin arziki ba.
Lawal masanin tattalin arziki ne ya rubuto daga Legas