Mahukunta a fannin aikin gona a kasar Malawi, sun bayyana yadda ake noman shinkafar kasar Sin a matsayin mai matukar muhimmanci, kuma abu muhimmanci wajen inganta noman hatsi a kasar dake kudancin Afirka.
Manyan jami’an ma’aikatar aikin gona na kasar Malawi ne suka bayyana hakan Juma’ar da ta gabata a Lilongwe, babban birnin kasar, a yayin rufe wani horo na aikin noman shinkafa na kwanaki 3 da tawagar kwararrun aikin gona ta kasar Sin suka shirya.
Horon yana daya daga cikin ayyukan da aka tsara, karkashin shirin ba da taimako na hadin gwiwar fasahohin aikin gona na kasar Sin a kasar ta Malawi.
Ya kuma hallara kusan malaman gona 40 da aka zabo daga sassan bunkasa aikin gona na kasar ta Malawi. (Mai fassarawa: Ibrahim)