Hukumar hana fasa kwauri ta kasa reshen jihar Katsina, kwastam ta kama wasu motoci guda takwas (8) da sauran kayayyaki wadanda kudinsu ya kai Naira miliyan ₦77,803,825 tsakanin watan Satumba zuwa Oktoban 2022.
Adadin kudin harajin motocin da aka kama ya kai ₦59,575,000.00 yayin da na sauran kayayyakin ya kai Naira ₦18,228,825.00.
Kwanturolan hukumar kwastam mai kula da jihar Katsina, Dalha Wada Chedi ne ya baje kolin wasu kayayyakin da rundunar ta kama a cikin wa’adin watanni biyun a hedikwatar rundunar da ke Katsina a safiyar ranar Litinin.
Ya ce daga ranar 1 zuwa 30 ga watan Satumban 2022, an tattara harajin naira miliyan ₦75,600,991.00 yayin da daga 1 ga watan Oktoba zuwa 31st 2022, aka tattara harajin naira miliyan ₦121,800,478.00.
A cewar Chedi, rundunar ta samu kudin haraji sama da Naira miliyan 500 daga ranar da aka sake bude kan iyakar Jibia, inda ya kara da cewa, an fitar da kayayyaki ta iyakar Jibia kawo yanzun na sama da Naira biliyan 5.
Ya yi nuni da cewa, Hukumar na karbar kudin haraji kan kayan abinci da ake shigowa dasu kasar ta kan iyakar Jibia kamar su Wake, Aya, Dabino, da gyada da sauran abubuwan da doka ta amince a shigo da su.