Hukumar hana fasa kwabri ‘kwastam’ (NCS) shiyyar ‘B’ da ke Kaduna ta cafke tare da kama kayayyaki nau’ika daban-daban da darajarsu (DPV) ya kai sama da naira biliyan daya a tsakanin watan Mayu zuwa Yulin 2023.
A sanarwar da jami’in watsa labarai na hukumar shiyyar B, Sufuritadan hukumar kwastam, Isah Sulaiman, ya ce, tsakanin watannin sun kame kaya 179 da darajar kudin duty dinsu (DPV) ya kai biliya daya da miliyan arba’in da hudu, dubu dari bakwai da saba’in da biyu, naira dari da hamsin da tara da kwabo gamanin (N1,044,772,159.80K).
Ya ce, an yi cafken ne a wurare daban-daban da suke karkashin kulawar shiyyar bisa amfani da samame na basira da hikima tare da kwarewar jami’ansu.
Ya ce kayayyakin da aka kama an haramta shigo da su da suka hada da motoci, shimkafar kasar waje da aka yi fasa kwabrinsu, kayan sawa da aka yi amfani da su na kasar waje, sabulan kasashen waje, mangyada da Pastas da dai sauransu.
A cewarsa, jami’an hukumar a shirye suke wajen cigaba da maida hankali kan ayyukan da ke gabansu na dakile dabarbarun masu fasa kwabri ta hanyar samun horo na musamman da mai rikon kwantirula-janar na hukumar, Bashir Wale Adeniyi ya sa gaba.
Sanarwar ta gargadi masu masu fasa kwabri da su sauya tunaninsu domin a cewarsa hukumar ba za ta taba barinsu su na cigaba da tafka ta’asa ba.