Kwanturolan hukumar kwastam (NCS) na shiyya ta daya (A), a ranar Laraba, ya ce sun kama kwali 1,700 na jabun tumatir wanda kudinsu ya kai Naira miliyan 50 da aka shigo da su kasar ba bisa ka’ida ba.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa, a shekarar 2019 ne gwamnatin tarayya ta haramta shigo da Tumatirin gwangwani ko na leda, hakan yasa ta kara haraji kan shigo da Tumatir daga kashi 5 cikin 100 zuwa 50 cikin 100 a wani yunkuri na tabbatar da cewa Hukumar Kula da Abinci da Kula da Magunguna (NAFDAC) ta tabbatar da lafiyar tumatirin.
A jawabin da ya yi wa manema labarai a Legas, kodinetan hukumar bangaren CGC, shiyya A, DC Mohammed Yusuf, ya ce baya ga tumatur na jabu da ya kai Naira miliyan 50.7, sun kama wasu kayayyaki irin su buhunan shinkafar waje; kayan gwanjo; Jarkunan man fetur (PMS); da motocin da aka yi fasakwaurinsu duk sun kai Naira miliyan 390.