• English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kyan Alkawari Cikawa

byCMG Hausa
3 years ago
Alkawari

Yanzu haka ana daf da cika shekaru 10 tun bayan taron farko na kwamitin kolin jamiyyar kwaminis ta kasar Sin na 18, tun bayan lokacin ne kuma sassan kasa da kasa ke zuba ido domin ganin yadda kasar Sin za ta dunkule tare da sauran sassan duniya, wajen cika alkawuran da ta dauka, na samarwa al’ummar duniya kyakkyawar makomar bai daya.

A iya cewa a bisa dukkanin shaidu “Kwalliya ta biya kudin sabulu”, domin kuwa kasar Sin ta shiga cikin hadakar kasashen duniya, wajen aiwatar da managartan shirye-shiryen samar da ci gaba, duk kuwa da kalubalen da duniya ta ci karo da su cikin wadannan shekaru.

  • Sin: Matakin Da Amurka Ta Dauka Babakere Ne Ta Fannin Kimiyya

Yayin ziyararsa ta farko a kasashen waje cikin watan Maris na shekarar 2013, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya zayyana burin kasarsa na bunkasa sabon salon cudanya, da hadin gwiwa da sauran sassan duniya, ta yadda za a kai ga cimma moriyar juna, wanda dukkanin bil adama zai ci moriyarsa.

Cikin shekarun baya bayan nan, kowa ya ga yadda kasar Sin ke kara azamar sauke nauyin dake wuyanta, na ingiza samar da ci gaba cikin lumana, da goyon bayan cudanyar sassa daban daban bisa adalci.

Sakamakon haka, mun ga yadda Sin ke ci gaba da ba da gudummawa a ayyukan wanzar da zaman lafiya da daidaito, da ba da gudummawar bunkasa raya tattalin arzikin duniya, da shiga ayyukan cimma moriyar bil adama na bai daya.

LABARAI MASU NASABA

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Tuni manufar dake kunshe cikin shawarar nan ta “Ziri Daya da Hanya Daya” ko BRI, ta shiga lungu da sassan duniya, inda ta samar da zarafi karfafa kawance, da dinkewar Sin da sauran sassan duniya a fannin samar da ci gaba.

Kaza lika Sin ta shiga ayyukan yaki da annobar COVID-19, ta samar da gudummawar kayan kandagarki da na rigakafin annobar, matakin da ya samu babban yabo daga sassa daban daban.
Duba da wadannan shaidu na zahiri, muna iya cewa, Sin ta cika alkawuran da ta dauka ga duniya, musamman ma ga kawayen ta makusanta wato kasashe masu tasowa. (Saminu Hassan)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci
Daga Birnin Sin

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?
Daga Birnin Sin

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025
Next Post
Gwamnatin Tarayya Ta Shiga Tsakani Kan Rikicin Da Ya Kunno Kai Tsakanin Gwamnatin Kogi Da Dangote

Gwamnatin Kogi Ta Bai Wa Dangote Sa'o'i 48 Ya Kulle kamfanin Simintinsa Da Ke Obajana

LABARAI MASU NASABA

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
A Kama Wani Likitan Bogi A Neja

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato Miyagun Ƙwayoyi A Jihar Jigawa

October 8, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

‘Yansanda Da Mutanen Gari Sun Daƙile Harin Boko Haram A Borno

October 8, 2025
…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio

‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio

October 8, 2025
Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Go to mobile version