Wasu bayanai na nuni da yara akalla 19 ne annobar cutar kyanda ta kashe a karamar hukumar Mubi ta Arewa a Jihar Adamawa.
Kwamishinan ma’aikatar lafiya na jihar, Felix Tangwami ya shaida haka ga manema labarai a Yola, ya ce sama da yara 200 ne suka kamu da cutar a karamar hukumar.
Ya ce an tabbatar da bullar cutar a jihar a ranar Asabar, wanda ya sa aka gaggauta tattara likitoci da magunguna ga al’ummomin da abin ya shafa.
Ya kuma bayar da tabbacin cewa za a mika yaran da suka kamu da cutar zuwa asibitocin da gwamnatin ta tanadar.
Kwamishinan ya ce tawagar likitocin za su tashi daga Mubi zuwa karamar hukumar Gombi inda aka samun bullar cutar.
Mista Tangwami ya dora laifin bullar cutar kan iyayen da ke kin yi wa ‘ya’yansu rigakafi kan barkewar cutar.
Haka kuma akwai rahoton bullar cutar shan inna, a karamar hukumar Gombi, to sai dai hukumomin jihar ba su kai ga tabbatar da rahoton ba.