ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, November 15, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kyautata Musayar Al’Adu Zai Toshe Duk Wata Kafa Ta Baraka Tsakanin Sin Da Afrika

by CMG Hausa
3 years ago
Afrika

An shiga makon tattauna batutuwan tattalin arziki da cinikayya da kuma hadin gwiwa da musayar al’adu tsakanin Sin da Afrika a lardin Zhejiang dake gabashin kasar Sin, a jiya Litinin, inda aka yi kira da zurfafa hadin gwiwar bangarorin biyu.

Zan iya cewa kasashen Afrika sun yi dace, inda wannan taro ke gudana jim kadan bayan kammalar taron kolin JKS karo na 20, inda Sin ta saita wata sabuwar akiblar neman ci gaba da zamanantar da kanta.

  • Xi Aike Da Wasikar Taya Murna Ga Taron Ilimi Karo Na 16 Na Cibiyoyin Kimiya Na Kasashe Masu Tasowa

Dacen da suka yi kuwa shi ne, akwai tarin sabbin darasin da ya kamata su dauka daga sabon tafarkin da Sin ta dauka na raya kanta, baya ga cin gajiyar kudurinta na kara fadada bude kofarta da habaka kasuwanci da kasashen waje.

ADVERTISEMENT

Wannan taro, kamar sauran tarukan da Sin kan shirya, wata dama ce ga kasashen Afrika ta jan hankalin kamfanonin kasar Sin su zuba jari ko fadada ayyukansu a kasashensu.

Kasashen Afrika na da albarkatu da ba a sarrafawa, kasar Sin kuma, na da tarin fasahohi da gogewa a fannin kirkire-kirkire, wanda zai zama hadin gwiwar moriyar juna, da zai kai kasashen Afrika ga amfani da dimbin arzikin da suke da shi, inda za su iya samun ci gaba har ma da kyautata rayuwar jama’a.

LABARAI MASU NASABA

Bangaren Sauka Na Kumbon Shenzhou-21 Ya Iso Doron Duniya

Sin Za Ta Mayar Da Martani Idan Har Japan Ta Aiwatar Da Matakin Da Bai Dace Ba

Sanin cewa kasar Sin babbar kasuwa ce, ba sabon abu ba ne, don haka fadada kasuwanci da kasar, babbar riba ce.

A irin wannan taro ne ya kamata kasashen Afrika su gano abun da ake bukata a kasar Sin kuma su hada gwiwa da kamfanonin kasar domin su taimaka musu fitar da hajojinsu da cin gajiyar babbar kasuwar kasar.

Duniya ta riga ta san yadda Sin take goyon bayan nahiyar Afrika, take kuma kara jan kasashen nahiyar a jiki domin su koyi dabarun raya kansu. Yadda ake kara zurfafa hulda tsakanin bangarorin biyu, na bukatar karin hadin gwiwa da musayar al’adu domin fahimtar juna ta yadda za a toshe duk wata kafa ta baraka a tsakaninsu, ta hakan ne kuma zuri’o’in Sin da Afrika na gaba, za su kasance tamkar ’yan uwa.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Bangaren Sauka Na Kumbon Shenzhou-21 Ya Iso Doron Duniya
Daga Birnin Sin

Bangaren Sauka Na Kumbon Shenzhou-21 Ya Iso Doron Duniya

November 14, 2025
Sin Za Ta Mayar Da Martani Idan Har Japan Ta Aiwatar Da Matakin Da Bai Dace Ba
Daga Birnin Sin

Sin Za Ta Mayar Da Martani Idan Har Japan Ta Aiwatar Da Matakin Da Bai Dace Ba

November 14, 2025
Jirgin Ruwan Dakon Jiragen Saman Yaki Na Sichuan Ya Fara Gwajin Sufuri A Karon Farko
Daga Birnin Sin

Jirgin Ruwan Dakon Jiragen Saman Yaki Na Sichuan Ya Fara Gwajin Sufuri A Karon Farko

November 14, 2025
Next Post
Hatsarin Mota Ya Halaka Mutum 37 Da Jikkata Wasu Da Dama A Hanyar Damaturu Zuwa Maiduguri

Hatsarin Mota Ya Halaka Mutum 37 Da Jikkata Wasu Da Dama A Hanyar Damaturu Zuwa Maiduguri

LABARAI MASU NASABA

NAF Ta Ragargaza Mafakar Ƴan Ta’adda A Zamfara, Ta Hallaka Dama-Dama

NAF Ta Ragargaza Mafakar Ƴan Ta’adda A Zamfara, Ta Hallaka Dama-Dama

November 15, 2025
Masu Kokarin Kashe Kansu Na Kara Karuwa A Nijeriya

Masu Kokarin Kashe Kansu Na Kara Karuwa A Nijeriya

November 15, 2025
Wakilai Daga Jihohi 19 Sun Isa Ibadan Don Taron PDP Na Ƙasa

Wakilai Daga Jihohi 19 Sun Isa Ibadan Don Taron PDP Na Ƙasa

November 15, 2025
Daliban FUTA 240 Sun Samu Digiri Mai Daraja Ta Daya

Daliban FUTA 240 Sun Samu Digiri Mai Daraja Ta Daya

November 15, 2025
Shakirat Ta Tsallaka Mataki Na Ƙarshe Na Zama Gwarzuwar Ƴar Wasan Afrika

Shakirat Ta Tsallaka Mataki Na Ƙarshe Na Zama Gwarzuwar Ƴar Wasan Afrika

November 15, 2025
Wasu Mahara Sun Kashe Mata 2, Tare Da da Ƙona Gidansu A Tudun Yola

Wasu Mahara Sun Kashe Mata 2, Tare Da da Ƙona Gidansu A Tudun Yola

November 15, 2025
Rundunar Sojin Nijeriya Ta Bayyana Dalilan Hana Jami’anta Auren ‘Yan Kasashen Waje

Rundunar Sojin Nijeriya Ta Bayyana Dalilan Hana Jami’anta Auren ‘Yan Kasashen Waje

November 15, 2025
Fashi Da Makami: An Yanke Wa ’Yan Nijeriya Hudu Mazauna Birtaniya Hukuncin Daurin Shekara 55 A Gidan Yari

Fashi Da Makami: An Yanke Wa ’Yan Nijeriya Hudu Mazauna Birtaniya Hukuncin Daurin Shekara 55 A Gidan Yari

November 15, 2025
Shugaban APC Na Kano Ya Nemi Afuwa Daga Al’ummar Fagge Kan Kalamansa

Shugaban APC Na Kano Ya Nemi Afuwa Daga Al’ummar Fagge Kan Kalamansa

November 15, 2025
‘Yansanda Sun Ceto Mutum 21 Da Aka Sace, Sun Kwato N4.8m Kuɗin Fansa

’Yansanda Sun Cafke Wani Da Ake Zargin Dan Ta’adda Ne A Jihar Kebbi

November 15, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.