Dan majalisar wakilai mai wakiltar kananan hukumomin Demsa, Numan da Lamurde a majalisar wakilai ta kasa, Honarabul Kwamoti B La’ori, ya bayyana kudurin ci gaba da ganin rayuwar ta kyautatu, a yankin da ma Jihar Adamawa baki daya.
Honarabul La’ori, ya bayyana haka lokacin da ya karbi bakuncin shugaban makarantar koyar da fasahar kere-kere da sana’o’in dogaro da kai, Nigerian Institute of Leather and Science Technology (NILEST) Zaria, Farfesa Ali Sani Muhammad, a ofishinsa da ke Abuja.
- Ba Za A Cimma Wannan Yarjejeniya Ba Tare Da Taimakon Sin Ba
- Matsalar Da Ta Haddasa Harin Bom Na Kaduna
Dan majalisar ya gode wa Farfesa Ali Sani, bisa goyon bayan da ya bayar na ganin an kai ga kafa cibiya ta makarantar NILEST a Numan, da kuma bada horon da aka yi wa matasa kan sana’o’in dogaro da kai na zamani.
A nasa jawabin, Farfesa Ali Sani Muhammad, ya yaba da himmar da Hon Kwamoti La’ori ke bai wa lamarin da ya shafi matasa, ya ce makarantar za ta ci gaba da hada hannu da shi (La’ori), na ganin ta samar da cikakken madogara domin kyautatuwar rayuwar matasa.
Haka kuma, DG Ali Sani, ya gode da samar da injin aikin buga takalma na zamani, da La’ori ya bai wa matasan da suka samu horo daga jami’an makarantar, ya ce zai tabbatar da aikin sabuwar makaranta a Numan, domin matasa su ci gajiyar kamar yadda tsarin yake.
A lokacin ziyarar, Hon Kwamoti La’ori, ya mika takardar shaidar mallakar filin gina sabuwar cibiyar makarantar NILEST a Numan.