Ubangiji ya fada cikin hakkin Annabi Yusuf, “Yusuf ya ce, ya sarki dora ni a kan taskar kasarka, ni masani ne mai kiyayewa.” Malamai suka ce, babu laifi in mutum Allah ya masa baiwa da wani abu ya fada, godiya ce ga ni’imar Allah, haka kuma wanda bai sani ba shi ma ya fada don kar ya hallakar da jama’a. Misali, mafarkin sarkin Misra da aka kira masu fassarar mafarki suka ce, ‘mafarkin sanyi ne kawai’ da masani Annabi Yusuf ya zo, sai ya bayyana cewa, tattalin arzikin Misra ne na shekaru Allah yake nuna wa Sarki.
Annabi Yusufa (AS), yana da wata Falala tun yana dan yaro da yana cikin kurkuku da yana kan sarauta, ake kiransa da Muhsini “Inna naraka minal muhsinin – lallali muna ganinka kana daga cikin masu kyautaye.”
- Kamannin Annabawa Suna Tukewa Ne A Siffofin Manzon Allah (SAW)
- Tausayi Da Kyawon Cika Alkawarin Annabi Muhammadu (SAW) II
Allah yake fada cikin Annabi Musa, “za ka same ni insha Allah mai hakuri”, Annabi Musa jarimi ne kuma mai hakuri, ya taba yin Azumi na kwana Arba’in amma da ya kama hanya yana neman Shehi (Mai tarbiyyantarwa) sai ga shi yana cewa “Atina gada’ana, lakad lakina min safarina haza nasaba – a kawo mana abincin ranarmu, gaskiya mun sha wahala a tafiyar nan.”
Allah ya fada a cikin Annabi Shu’aibu, inda yake cewa, Ya Musa “satajiduni in sha Allah minas salihin – ni kuma za ka same ni in sha Allah daga cikin managarta masu nasiha,” (in ka yi min kiwon shekara 10 na aura maka ‘yata).
Allah ya kara fada cikin Annabi Nuhu, “wama uridu an ukalifakum ila ma an hakum anhu, in uridu illal islaha mastada’atum, wama taufiki illa billah, alaihi tawakkaltu wa ilaihi unib – ba ina so in saba muku ba ne cikin abin da na hane ku da shi (in hana ku ni kuma in koma daki in ta aikatawa), gyara nake nema iya karfina, wurin Ubangijina nake neman dacewa, a gare shi na dogara kuma shi ne makomata.”
Ubangiji ya fada cikin Annabi Ludu, “wa Ludan a tainahu hukman wa ilman, innahum kanu yusari’una filkairati wa yad’unana ragaba wa rahaba, wa kanu lana kashi’in – lallai mun ba wa Annabi Ludu Annabta da Ilimi. Dukkan Annabawa sun kassance masu tsere cikin isar da aikin alkairi, kuma suna kwadaitarwa da tsoratarwa zuwa gare mu, kuma masu kankan da kai ne a gare mu.” Sufyannussauri ya ce, ma’anar Annabawa suna rige-rige wurin aikin alkhairi, shi ne, bakin cikin da suke ciki dawwamamme na son shiryar da halitta.
Allah tabaraka wa ta’ala ya bayyana cikin Ayoyi da yawa na ambatar kyawawan halin Annabawa wacce take shiryarwa bisa cikarsu. Ya zo a cikin Hadisai masu yawa na yabon halin Annabawa, kamar fadinsa mai tsira da aminci, “Annabi Yusufa babba ne dan babba dan babba dan babba (Yusufa dan Yakubu dan Ishak dan Ibrahimu).”
Shi kuma Annabi (SAW), girma ya kare a kansa. Alkadi Iyad ya ruwaito Hadisin Abdullahi bin Abbas yayin da yake fassara ‘watakallubaka fissajidin – da jujjuyawarka a cikin masu sajjada’ yana cewa, “Daga Annabi zuwa Annabi har na fitar da kai Annabi.” A wani misali da za mu bayar, da ya shafi hakkin Darikar Tijjaniya, shehu Ibrahim Inyas yake cewa, babba dan babba dan babba, shi ne ‘Shaikhani’ – Shaikhani dan Muhammadu Manna dan Muhammad Dulba dan Ahamdu Abba dan Muhammadul Hafaz wanda ya dauko Darika daga shehu Tijjani, amma albarkacin Faila, ko kallon nasabarsa ba ya yi.
An ruwaito cewa, lallai Annabi Sulaiman tare da abin da Allah ya ba shi na Mulki amma bai kallon sama sabida kankan da kai ga Allah, ya kasance yana ciyar da Mutane dadadan abinci amma shi kuma ya ciyar da kanshi Gurasar Gero. An yi wahyi ga Annabi Sulaiman, Allah ya kira shi da cewa, “Ya shugaban masu Ibada, ya dan wanda duk masu ibada ke ko yi da shi (Dawud).” Duk da mulkin Annabi Sulaiman amma tsohuwa takan tsayar da tawagarsa ta Aljanu a kan Iskar da ke daukarsa zuwa wurare a kan hanya ta yi masa magana. Annabi Sulaiman, a fadarsa duk wanda bai gani ba sai ya gane, wata rana ya duba bai ga Huda-huda ba sai da ya tambaya ina ya shiga.
Wata kila an ce wa Annabi Yusufa, me ya sa kake jin Yunwa? Gashi kuma kai ne ministan tattalin arzikin kasa, sai ya ce, “ina tsoron in koshi sai in manta da mai jin Yunwa.”
Abu Hurairah ya ruwaito daga Annabi (SAW) yana cewa, “Allah ya saukake wa Annabi Dawuda littafin Attaurarsa, ya kasance yana horo a dora masa sirdi a kan abin hawansa, kafin a gama dorawa ya gama karanta attaurarsa.” Allah ya ba wa Al’ummar Annabi (SAW) irin wannan mu’ujiza, akwai masu Takarar Alkur’ani Hizfi 60 a sa’o’i biyu, yana daga cikin Karamar Shehu Tijjani Abul-abbas, dayyun Kur’ani daga farkon Kiran sallah zuwa karshe. An ruwaito cewa, Sayyadina Ali yana saukar Alkur’ani 70,000 cikin dan lokaci.
Annabi Dawudu, ba ya cin abinci sai wanda ya yi sana’a da hannunsa ya samu ko ya siya.
Ubangiji tabaraka wata’ala ya fada ga Annabi Dawudu “mun tausasa masa karafa.” A wata aya kuma Allah ya hore shi da ya yi rigar yaki – sulke da fadinsa cewa, “ka yi sulke, kuma ka yi sakar mai kyau.” Annabi Dawud ya roki Ubangiji ya azurta shi da Sana’a ta yadda ba sai ya nemi komai a Baitulmali ba.
Wata rana, wani abu ya hada Sayyadina Ali da Khalid bin Walid takaddama, Sayyadina Ali ya dauko karfen da mata ke nika da shi ya rataya wa Khalid a wuyansa kuma babu yadda za a yi a cire sai an narka karfen, Khhlid ya kai kara ga Khalifa, Sayyadina Abubakar, nan take ya aika a kira Sayyadina Ali, da zuwansa, sai Khalifa ya roke shi da ya cire karfen da ya rataya wa Khalid don bai da karfin da zai iya cirewa, take ya fara babballa karfen har ya fita gaba daya. Wanda ba Waliyyi ne mai karama ba sai ya yi Sana’a ya koya yadda ake sarrafa karfe, duk nauyin karfe in aka sa shi a wuta sai ya zama mai taushi.
Annabi Dawudu ya kasance yana raba darensa biyu – ya yi barci a kashin farko ya yi ibada a kashin karshe, Azuminsa ya kasance, yana shan ruwa kwana daya ya yi azumi kwana daya. Annabi Dawud ya kasance yana sa rigar gashin tumaki. Yana shimfida da fata ko gashin dabbobi, yana cin wainar Gero da gishiri wacce take da sauran tokar wuta a jikinta, yakan cakuda abin shansa da hawaye sabida yawan hawayen da ke futa a idanunsa.
Ba a kara ganin dariyarsa ba tun lokacin da Allah ya zarge shi da kuskure irin na Annabawa (lokacin da Mala’iku biyu suka zo masa a siffar mutane suna takaddama kan dabbobi, yana da guda 99 amma yana son kwace wa mai guda daya ya hada ta cikin 99 da yake da su), bai kuma kara daga kansa sama ba sabida kunyar Ubangijinsa, bai gushe ba yana kuka tsawon rayuwarsa.
Wata kila an ce, Annabi Dawuda shi ne farkon shugaban kasa da yake fita a asirce yana tambayar ‘yan kasa kan halin shugabansu.
Wata kila an ce da Annabi Isah dan Maryam sabida yawan tafiya a kasa, “da ka riki Jaki” sai ya ce, ina da girma a wurin Allah da har sai ya shagalantar da ni da Jaki. Annabi Isah ya kasance yana saka buzu ajikinsa, yana cin tsirrai, irin su kulubutu da irya da dai sauransu, bai kuma taba mallakar gida ba, duk inda bacci ya riske shi a nan zai kwanta, ya fi son a kira shi da ‘Talaka’.