Gwamnan Jihar Gombe kuma shugaban kungiyar Gwamnonin Arewa, Muhammadu Inuwa Yahaya ya ce, matsalar da ta addabi hanyar Gombe zuwa Bauchi na yawan rugujewar gadoji da kuma yankewar hanyar sun sa hanyar ta zama tarkon mutuwa ga matafiya a Arewa Maso Gabas.
Don haka, ya yi kiira da babban murya ga Gwamnatin tarayya ta dauki matakin gaggawa don magance matsalar cikin kankanin lokaci.
Hanyar ce dai ta hade Jihohin Gombe da Bauchi da Taraba da wasu yankunan Jihar Borno, hakan yasa ta kasance muhimmiya ga harkokin sufurin kayayyaki da zirga-zirgar jama’a.
A ziyarar gani da ido da ya kai wurin da gadar ta yanke a Kalajanga na karamar hukumar Kirfi ta Jihar Bauchi a jiya, Gwamna Inuwa ya jaddada muhimmancin hanyar ga harkokin tattalin arziki da zamantakewar al’ummar yankin Arewa Maso Gabas.
Gwamnan ya kwatanta hanyar a matsayin wata muhimmiyar jijiyar dake hade muhimman yankunan kasar nan, ya na mai bayyana muhimmiyar rawar da take takawa a harkokin tattalin arzikin jama’ar yankin.
“Wannar hanya kamar jijiya ce dake hada zuciya da kwakwalwa, wacce ke samar da jini da iskar numfashi, idan ta yanke babu wani bangare na jiki da zai iya aiki, wannan ita ce hanyar da take zuwa wannan yanki daga sassan kasar nan.”
Ya kara da cewa “Na yi imanin cewa gwamnan Bauchi ya na nan, kuma kar ku yi mamaki gobe ku ga gwamnan Adamawa ko Borno a nan saboda mahimmancin wannar hanyar ga dokacin wannan yankin.”
Ya kuma jaddada bukatar gyara da sake gina hanyar, inda ya ce hanyar ta kusan shekaru 50 da ginawa, don haka tana bukatar karin gadoji da garanbawul baki daya.
Gwamna Inuwa ya ce zagayawa ta wasu hanyoyi yana tattare da marin kashe kudi da bata lokaci, yana mai jaddada bukatar kammala aikin gyaran cikin gaggawa don saukaka zirga-zirgar ababen hawa a fadin jihohin na Arewa Maso Gabas.
Gwamnan ya kuma jaddada muhimmancin hanyar ga ci gaban tattalin arziki da zamantakewa ba ga Jihar Gombe kadai ba, har ma da yankin arewa maso gabas baki daya, yana mai alakanta rashin kyan hanyar ga matsalolin muhalli da karuwar aikace-aikacen jama’a.
Ya ce tun bayan hawansa mulki yake ta bin diddigin yadda hanyar za ta samu gyaran da ya kamata.
“A baya na ziyarci ma’aikatar ayyuka kusan sau hudu kan wannan batu, ina kokarin jawo hankalin Gwamnatin tarayya kan ta dauki matakin gaggawa don magance wannar matsala kwata-kwata. Ko a jiya ma sai da na kira Babban Sakataren Ma’aikatar Ayyuka na Tarayya kan batun.
“Dole ne Gwamnatin Tarayya ta shigo cikin lamarin da gaggawa ta magance wannar matsala saboda rayuwar miliyoyin jama’a ta ta’allaka da wannar hanya”, yana mai bayyana lamarin a matsayin wadda ke buƙatar daukin gaggawa.
Gwamna Inuwa ya kuma yi alkawarin kara kaimi ga shugaban kasa, don samar da mafita ta din-din-din ga matsalar.
Da yake yabawa da ayyukan da hukumar kula da hanyoyi ta tarayya (FERMA) ke ci gaba da yi na kokarin samar da mafita ta wucin gadi, ya bayyana fatan cewa hakan zai sa a samu mafita cikin ‘yan kwanaki.
Da yake jawabi a madadin ma’aikatar ayyuka ta tarayya, jami’in ma’aikatar dake kula da aikin, Engr. Bitrus Dauda, ya ce ma’aikatar na yin duk mai yiwuwa don gyaran hanyar, tare da bada tabbacin kara matsin lamba kan bukatar gina karin gadoji a kan hanyar.
Ya ce, “Tun ba yau ba muka mika koke ga ma’aikatar ayyuka ta tarayya kan yanayin hanyar musamman wuraren da ake bukatar manyan gadoji, yanzu muna jiran a ba mu tsarin aikin ne don aiwatar da shi”.
Shi ma a nasa jawabin, kwamandan hukumar Kiyaye Hatsurra ta Tarayyar Reshen Jihar Bauchi, Mista Patrick Ikaba, ya ce rundunar ta kammala shirye-shiryen sanya alamun gargadi da ankararwa a wurare masu mahimmanci don magance hatsura, tare da shawartar masu ababen hawa da sauran masu amfani da hanyar su koma bin wassu hanyoyin daban don kare lafiya da rayukansu.
Yankewar gadan na baya-bayan nan ya faru ne a ranar Lahadi bayan da aka shafe sa’o’i ana ruwan sama kamar da bakin kwarya, wanda ya yi sanadiyar ambaliyar ruwa da ta fi karfin gadar.