Babbar Na’urar wutar lantarki ta Nijeriya da ke karkashin kulawar kamfanin samar da wutar lantarki na kasa (TCN) ta tsaya cak da aiki a sanyin safiyar ranar Alhamis, lamarin da ya jefa kasar baki daya cikin duhu.
Binciken da LEADERSHIP ta gudanar a kan layukan samar da wutar lantarkin ya nuna cewa, da misalin karfe 7:00 na safiya, megawats 48.50 kacal ya rage wanda hakan ke nuna cewa, layuka biyu ne ke aiki cikin 27 da ke bayar da wutar lantarkin.
Wannan na zuwa ne mako guda bayan da TCN ta yi bikin cika kwanaki 400 layukan suna bada wuta ba tare da tangarda ko katsewa ba.
Kamfanonin Rarraba wutar da dama sun tabbatar da cewa, Babbar Na’urar samar da wutar lantarki ta kasa ta katse da misalin karfe 12:41 na dare.