Wasu rahotanni da cibiyar nazari ta kasa da kasa ta Arab Barometer ta fitar a baya bayan nan, sun nuna cewa, galibin Larabawa sun yanke kauna da ingancin tsarin demokradiyyar yammacin duniya, kana an samu karin masu sha’awar tsarin kasar Sin.
Nazarin da aka gudanar a kasashe 9 da suka hada da Masar da Tunisia da Iraqi da Sudan da Libya da Jordan da Lebanon da Mauritania da Palastine, sun shafi mutane 23,000. Kuma bisa wannan nazari, cibiyar Arab Barometer ta fitar da wasu rahotanni biyu a shafinta na website a farkon wannan wata, daya mai taken “Tsarin Demokradiyya a Gabas ta Tsakiya da Arewacin Afrika” yayin da taken dayan shi ne “Ra’ayin Jama’a kan Takarar Sin da Amurka a Gabas ta Tsakiya da Arewacin Afrika”.
Rahotanni sun ruwaito cewa, cikin shekaru 10 da suka gabata, musamman shekaru 5 da suka wuce, mutane a kasashen Larabawa a Gabas ta Tsakiya da arewacin Afrika, na kara shakku game da alfanun tsarin demokradiyyar yammacin duniya, kuma karin mazauna kasashen sun yi ammana cewa, tsarukan demokradiyyar yammacin duniya ba su dace da raya tattalin arziki da tabbatar da zaman lafiyar al’umma ba, haka kuma ba sa ingiza gwamnati daukar matakan da suka dace. (Fa’iza Mustapha)