Lardin Hunan na tsakiyar kasar Sin, ya yi gwajin biyan kudi da takardun kudin Sin kai tsaye zuwa na kasashen Afrika, domin taimakawa kasashen saukaka matsin musayar kudaden ketare saboda karancinsa.
Lardin na Hunan ya kammala wasu kananan yarjeniyoyin 12 na bani gishiri in baka manda da kasashen Afrika 4 a cikin shekarar 2021.
Kuma bisa nasarar da aka samu, sassan kula da shige da fice da haraji da musayar kudaden ketare na lardin, sun gabatar da kudurin gwajin biyan kudin cinikayya a tsakanin bangarorin biyu da takardun kudadensu kai tsaye.
Yang Yi, jami’i a ofishin kula da cinikayya na lardin Hunan, ya ce ana sa ran sabon tsarin zai fadada shigar kayayyakin Afrika cikin kasar Sin tare da karfafawa kamfanonin Sin gwiwar yin kasuwanci da takwarorinsu na Afrika. (Fa’iza Mustapha)