Lardin Zhejiang mai tafiyar da harkokin raya tattalin arziki, dake kudu maso gabashin kasar Sin, ya shirya gina wata cibiyar samarwa da cinikayyar manyan hajojin da ake fitarwa ketare, a cikin yankinsa na ciniki mara shinge.
Bisa wani shiri da ma’aikatar kula da cinikayya da gwamnatin lardin suka fitar, zuwa shekarar 2030, jerin tsibiran dake cikin yankin cibiyar, za su zama masu gudanar da ayyukan da za su mamaye baki dayan tsarin ayyukan masana’antun da ya hada da samar da wurin ajiya da na jigila da nazari da harkokin da suka shafi sufurin ruwa da cinikayya da harkokin kudin.
Har ila yau, bisa shirin, cibiyar za ta kunshi yankin da zai mayar da hankali kacokan kan cinikayyar manyan hajojin. Haka kuma zai karfafawa bankunan ketare gwiwar bude rassansu a wurin da kuma taimakawa bankuna wajen samar da hidimomin da suka shafi cinikayyar manyan kayayyaki. (Fa’iza Mustapha)