Jama’a masu bibiyarmu a wannan shafi na Ado Da Kwalliya assalamu alaikum. Idan ba a manta ba a makon da ya gabata mun fara kawo muku bayani a kan yadda ake kawata falo da launuka masu kayatarwa, a wannan makon ma za mu ci gaba inda za mu kawo muku bayani a kan launukan da ake yayi daya-bayan-daya.
Kore
A bana ana ma wannan launi kirari da “karshen kayan ado mai ban sha’awa da za a kawata falo da shi”.
Kore shi ne shahararren launi na falo da ake yayi a wannan shekarar ta 2022.
“Wasu masu sana’ar kayan ado na cikin gida sukan hada kore da sauran kayan alatu da ake kawata falo da su kamar su kayan da aka sarrafa da katako da sauran abubuwa masu inganci domin launin ya bayar da ma’ana mai ban sha’awa,” in ji masanin kwalliya Mista Ben.
Wasu kuma sukan nemi karin launuka da za su bayar da sha’awa mai ban mamaki, musamman kamar hada shafa launin kore a bangon tare da samar da kanana da manyan kujeru da suke da launin da zai saje da kore.
Ruwan Toka-toka (Grey)
“Wannan wani launi ne mai ban sha’awa, yana samar da yanayin mai kyau wanda za a iya fadadawa da kayan ado na ‘palette’,” in ji Kelly Collins, wani kwararren mai zanen ado kuma shugaban sashen kere-kere na Kamfanin Swyft Home.
“Launuka masu saisaita zukata (ruwan bula da launin toka) za su dace da launin toka-toka a cikin falo. Haka nan idan aka hada da abubuwan ado irin su ‘terracotta’ ko ‘burgundy’, za su inganta kyawon launin na ruwan toka-toka da kawo gamsuwa a falo.” In ji masanin.
Launin Shudi (Kakin Sojojin ruwa)
Launukan shudi daban-daban kan bayyana sosai a cikin jerin launukan da aka fi so, haka nan launin ‘inky’ na kara zama mashahuri idan aka hada shi da shudi. “Ka tuna cewa launin shudi ya dace da launuka masu yawa kuma yana sanya yanayi ya zama mai kwantar da hankali. Idan kuna son samar da falo mai kuzari da zai karfafa ganin mai gani ya kalla ya kara kallo, a yi amfani da launin Shudi, “in ji Kelly.
Teal
Launin ‘Teal’ yana da dan cika ido fiye da shudi mai haske, ida aka yi amfani da launin lemu mai dan duhu ko mai ratsin ja zai iya kara bayyana shi. Teal zabi ne mai kyau musamman idan kuna son yin ado da kayan gargajiya.
Bulu
“Amfani da abubuwa masu launin bulu yana kara birge mutanen da ke son kawo alamomi na duniyar halitta a cikin gidajensu,” in ji Ben.
“Bulu launi ne mai kwantar da hankali da saisaita zuciya, sannan yana kara zurfafa tunanin wanda bulu yake birge shi . Tun da yawancin mu yanzu suna aiki daga gida sau da yawa, wannan ya sa bulu ya zama babban launin da ya kamata a yi ado da shi.” In ji shi.
Mu tara mako na gaba cikin yardar Allah.
Mun samo daga: https://www.countrylibing.com/uk/