• English
  • Business News
Monday, October 27, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Launukan Kawata Falo Na Zamani

by Bilkisu Tijjani
2 years ago
Falo

Jama’a masu bibiyarmu a wannan shafi mai matukar farin jini da albarka, ina yi muku sallama irin ta Addinin Musulunci.

Assalamu alaikum Warahmatullah Ta’ala Wabarakatuhu, da fatan kuna cikin koshin lafiya. A wannan makon za mu fara kawo muku tsaraba ce daga irin launukan da ya dace a kawata falo da su a zamanance.
Na san yana daga cikin burin kowace mace ta ga ta tsara falon gidanta yadda duk wanda ya gani zai yi sha’awa musamman maigida ran gida.

  • Yadda Uwargida Za Ta Yi Kwalliyar Gida Da Sallah

Launin Kore (Green), Launin Toka-toka (Grey), da Launin Kakin Sojojin Ruwa su ne suka zama mashahurai da ake amfani da su wajen kawata falo a wannan zamanin. Sabon bincike na Shafin Swyft Home, ya gano cewa jama’a masu son ado su kan yi zabi mafi dacewa a abubuwa da yawa na rayuwarsu musamman batun launuka na kaya ko fentin gida da za su kawata gidajensu su yi kyau da ban sha’awa.

Ba abin mamaki ba ne cewa launin toka ya kasance mai farin jini na biyu baya ga Kore da ya sha gabansa, yayin da sauran wasu launukan kamar shudi su ma suka kasance masu ba da sha’awa.

Sai dai duk da cewa launin Kirim (Cream) da Fari (White) ba su yi wani farin jini na a-zo-a-gani ba zuwa yanzu a shekarar nan ta 2023 (kamar yadda masana kwalliya suka yi hasashe), ruwan hoda da rawaya kuwa, sun samu karin karbuwa.

LABARAI MASU NASABA

Yadda Za A Magance Amosanin Baki

Hadin Tsumin Baure

“Kore (Green) shi ne launin da aka fi ya yi a falo tun daga farkon shekarar 2023, don haka ya zama a matsayi na daya saboda yadda ake neman sa don kawata launin falo,” in ji Ben White, masanin kwalliya da kasuwanci a shafin Swyft Home.

“An yi hasashen farin jinin da launin kore zai yi a tsakanin masana kwalliya da masu kwata adon gida tun kafin shekarar 2021, don haka ya zama shi ake yi a yanzu wajen kawata falo don ya yi kyawon gani. Ina ga abin da ya sa launin kore ya samu irin wannan karbuwa da farin jini shi ne, akwai mutanen da suke son ganin launin waje (na shuke-shuke da ciyayi) ya shigo cikin gidajensu.”

“Hada launuka masu ban sha’awa da kayatarwa shi ne babban abin lura wajen kawata gida a wannan shekarar. Shi ya sa masana kwalliya suka fi mayar da hankali a kan hade launukan da za su fi dacewa da juna a tsakanin fentin da za a yi wa falo da kayan da za a zuba a falon kamar kujeru da sauransu don falon ya zama ya tsaru yadda ya kamata.” In ji shi.

Akwai dai launuka guda 10 da za mu kawo muku su daya-bayan-daya da ake yayi wajen kawata falo a zamanin nan.

Don haka mu hadu a mako mai zuwa domin ganin, shin wadanne launuka ne wadannan?
Mun samo daga: https://www.countrylibing.com/uk/

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Yadda Za A Magance Amosanin Baki
Ado Da Kwalliya

Yadda Za A Magance Amosanin Baki

October 4, 2025
Hadin Tsumin Baure
Ado Da Kwalliya

Hadin Tsumin Baure

September 27, 2025
Gyaran fuska
Ado Da Kwalliya

Gyaran Fuska Da Laushin Fata

August 30, 2025
Next Post
An Ƙaddamar Da Shirin Yaƙi Da Rikicin Ƙabilanci A Jihar Filato

An Ƙaddamar Da Shirin Yaƙi Da Rikicin Ƙabilanci A Jihar Filato

LABARAI MASU NASABA

Gwamnati Za Ta Fara Sayar Wa Ɗangote Ɗanyen Mai Da Naira A Watan Oktoba

Ba Za A Samu Ƙarancin Man Fetur A Lokutan Bukukuwan Ƙarshen Shekara Ba – Dangote 

October 27, 2025
An Zaɓi Birgediya Janar Yake A Matsayin Sarkin Sayawa Na Farko Duk Da Zanga-zanga 

An Zaɓi Birgediya Janar Yake A Matsayin Sarkin Sayawa Na Farko Duk Da Zanga-zanga 

October 27, 2025
Falo

Tsohon Gwamnan Jigawa, Lamido Ya Bayyana Aniyar Takarar Shugabancin Jam’iyyar PDP Na Ƙasa

October 27, 2025
Sojoji Sun Kashe ‘Yan ta’adda 10, Sun Ƙwato Makamai A Borno

Sojoji Sun Kashe ‘Yan ta’adda 10, Sun Ƙwato Makamai A Borno

October 27, 2025
Hatsarin Jiragen Ruwa

Matasa 5 Sun Mutu A Hatsarin Jirgin Ruwa A Gombe

October 27, 2025
Tunawa Da Dawowar Taiwan Kasar Sin Shekaru 80 Da Suka Wuce Yana Da Ma’ana Sosai

Tunawa Da Dawowar Taiwan Kasar Sin Shekaru 80 Da Suka Wuce Yana Da Ma’ana Sosai

October 26, 2025
Matatar Dangote Za Ta Faɗaɗa Ƙarfin Aiki Zuwa Ganga Miliyan 1.4 Kullum

Matatar Dangote Za Ta Faɗaɗa Ƙarfin Aiki Zuwa Ganga Miliyan 1.4 Kullum

October 26, 2025
Kara Bude Kofofin Sin Zai Samar Da Karin Gajiya A Fannin Bunkasar Duniya

Kara Bude Kofofin Sin Zai Samar Da Karin Gajiya A Fannin Bunkasar Duniya

October 26, 2025
“Ba Gudu Ba Ja Da Baya Game Da Tsarin “Call-up system” A NPA”

“Ba Gudu Ba Ja Da Baya Game Da Tsarin “Call-up system” A NPA”

October 26, 2025
Ya Zuwa Satumban Bana Adadin Lantarki Da Sin Ta Samar Ya Karu Da Kaso 17.5%

Ya Zuwa Satumban Bana Adadin Lantarki Da Sin Ta Samar Ya Karu Da Kaso 17.5%

October 26, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.