Wasu manyan jami’an kasar Habasha sun bayyana cewa, layin dogon da ya sada tsakanin kasar Habasha da Djibouti da kasar Sin ta gina, yana kara inganta bangaren hada-hadar kayayyaki na kasar Habasha, kana ya zama wani muhimmin ginshiki da ke taimaka wa cinikayyar shigo da kaya da fitar da su zuwa kasashen waje a kasar.
Jami’an sun bayyana hakan ne a wata ganawa da suka yi tare da masu ruwa da tsaki a harkar sufuri da shigo da kayayyaki da fitar da su waje na kasar Habasha, a ranar Asabar da ta gabata.
Da yake jawabi a wajen taron, ministan sufuri da hada-hadar kayayyaki na kasar Habasha, Alemu Sime ya bayyana cewa, kasar da ke gabashin Afirka tana aiki tukuru don zamanantar da fannin sufuri da hada-hadar kayayyaki, a wani bangare na burin da ta sa a gaba wajen kawo sauyi ga harkokin cinikayyar shigo da kayayyaki da fitar da su waje.
Ya ce, layin dogo da ya sada tsakanin kasar Habasha da Djibouti mai tsawon kilomita 752, yana kara kaimin tabbatar da cikar burin kasar, yana mai bayyana muhimmancin ingantawa da fadada samar da harkokin sufurin ababen hawa da kayayyaki, tare da mayar da hankali musamman a kan layukan dogo. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp