Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Leicester City dake buga babbar gasar Firimiya ta kasar Ingila ta koma gasar yan dagaji ta Championship bayan da tayi rashin nasara a guda a wasanta da Liverpool.
Leicester wadda ta lashe gasar Firimiya a shekarar 2016 ta samu maki 18 kacal a wasanni 33 da ta buga, ta zura kwallaye 27 yayinda aka zura mata kwallaye 73 a ragarta, Leicester ta koma gasar Championship duk da cewar akwai sauran wasanni 5 da su ka rage ba a buga ba a gasar Firimiya ta bana.
- Yaushe Liverpool Za Ta Lashe Gasar Firimiyar Ingila?
- Salah Ya Kafa Tarihi Yayin Da Liverpool Ke Dab Da Lashe Gasar Firimiya
Kocin Leicester Ruud Van Nistelrooy ya karbi ragamar horarwar Leicester a watan Janairu bayan raba gari da kungiyar ta yi da Steve Cooper, amma kuma abinda ake gujewa ya faru ga kungiyar wadda ke matsayi na 19 akan teburin gasar Firimiya.
Trent Alexander Arnold ne ya ci wa Liverpool kwallonta, wadda kuma ta kasance kwallo daya tilo a aka ci a wasan, zuwan Leicester gasar yan dagaji ya sa ta kasance kungiya ta biyu da ta koma bayan Southampton a bana.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp