Ƙungiyar ƙwallon kafa taLeicester City dake buga gasar Firimiya ta ƙasar Ingila ta kori kocinta Steve Cooper yayinda ƙungiyar ta ke matsayi na 16 teburin gasar Firimiya bayan buga wasanni 12.
Chelsea wadda tsohon kocin Leicester Enzo Maresca ke jagoranta ta doke Foxes da ci 2-1 a yau Asabar, rashin nasarar da ta samu ya sa mahukuntan ƙungiyar su ka ɗauki wannan mataki.
Cooper ya karɓi ragamar ƙungiyar daga Maresca bayan dan ƙasar Italiyar ya jagoranci Leicester ta lashe kofin ƴan dagaji na Championship na shekarar 2023-24 kuma ya dawo da su gasar Premier.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp