Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya aika wa taron kaddamar da alkaluman kididdigar kirkire-kirkire na Duniya na shekarar 2022 na hukumar dake sa ido kan ikon mallakar fasaha ta kasa da kasa wato WIPO a takaice wasikar taya murna a jiya Alhamis.
Li Keqiang ya bayyana cewa, kirkire-kirkiren kimiyya shi ne babban karfi dake inganta ci gaban al’ummar bil’adam. Sin tana dora muhimmanci sosai kan kirkire-kirkiren kimiyya, da hada kai a bangaren ayyukan kirkire-kirkire na kasa da kasa, da kare ikon mallakar fasaha, da karfafa hadin gwiwar kasa da kasa game da kirkire-kirkiren kimiyya a dukkan sassa. Ya zuwa yanzu, karfin kimiyya da fasaha da fannin kirkire-kirkire na kasar Sin, ya samu babban ci gaba.
Li Keqiang ya nuna cewa, a nan gaba, kasar Sin za ta kara bude kofa da nufin karfafa mu’amala da hadin gwiwar kasa da kasa, da shiga harkokin kimiyya da fasaha na kasa da kasa, da ci gaba da fadada fannonin hadin gwiwar kirkire-kirkire na duniya, da neman samun bunkasuwa cikin hadin gwiwa, da hada kai da kasashe don gina gidaje masu kyau ga daukacin bil-adam.
Sin tana son ci gaba da yin hadin gwiwa tare da hukumar WIPO, da kokarin kafa ka’idojin mallakar fasaha na kasa da kasa ba tare da wata rufa-rufa ba, bisa daidaito da inganci.
Alkaluman kididdigar kirkire-kirkire na duniya na shekarar 2022 da hukumar WIPO ta fitar a jiya Alhamis sun nuna cewa, matsayin kasar Sin a fannin kirkire-kirkire a duniya, ya ci gaba da bunkasa a ‘yan shekarun nan, inda ya kai matsayi na 11 a shekarar 2022.( Mai fassara: Safiyah Ma)