Firaministan kasar Sin Li Qiang ya bayyana cewa, a matsayin kasar Faransa na mambar din-din-din a kwamitin sulhu na MDD, kana babbar abokiyar hulda ce ta kasar Sin bisa manyan tsare-tsare, kuma alakar dake tsakanin Sin da Faransa ta kai babban mataki na ci gaba kuma tana da muhimmanci a duniya, wanda ya dara matakin alakar kasashen biyu.
Li wanda ya bayyana hakan a lokacin da ya isa birnin Paris domin ziyarar aiki a Faransa, ya kuma bayyana cewa, a shirye kasar Sin take ta yi aiki tare da kasar Faransa wajen kara bude kofa ga juna, da kara karfin juriyar masana’antu da samar da kayayyaki tsakanin Sin da Faransa da kuma tsakanin Sin da Turai, da zurfafa mu’amala da fahimtar juna tsakanin al’ummomin kasashen biyu, da yin koyi da juna, da magance kalubalen da duniya ke fuskanta kamar matsalar sauyin yanayi, da samun ci gaba mai dorewa, ta yadda za a samar da wani sabon kuzari ga ci gaban alakar dake tsakanin Sin da Faransa mai dorewa, da kara azama da karfin gwiwa wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da ci gaba a duniya baki daya.(Ibrahim)