Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya bayyana a yau Alhamis cewa, cikin shekaru 10 da suka gabata, kasar Sin ta samu jerin muhimman sakamako a kokarinta na gina alumma mai makoma ta bai daya ga daukacin bil adama.
Li Qiang, ya bayyana haka ne cikin muhimmin jawabin da ya gabatar yayin bikin bude taron shekara-shekara na dandalin tattaunawar harkokin Asiya na Boao na bana.
A cewarsa, yayin da ake fuskantar yanayi na rashin tabbas, kwarin gwiwar da kasar Sin ke da shi ya kasance jigo wajen kiyaye zaman lafiya da ci gaba a duniya, abun da aka gani da gaske a baya, kuma ake kara gani a yanzu da har ma da nan gaba.
Ya ce kasar Sin za ta nace ga aiwatar da yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga waje da neman ci gaba bisa kirkire-kirkire, ba tare da laakari da sauyin da duniya za ta samu ba.
Ya kara da cewa, Sin za ta gabatar da jerin wasu sabbin matakai na fadada samun damar shiga kasuwarta da inganta yanayin kasuwanci da saukaka aiwatar da ayyuka.
Ta hakan a cewar firaminstan, ba ingiza sabon karfi da kuzari ga tattalin arzikin duniya kasar Sin za ta yi ba, har ma da samarwa duniya damarmaki tare da hanyar cin gajiya daga ci gaban kasar.
Sannan a yayin zaman tattaunawa tsakanin wakilan ’yan kasuwar Sin da na kasashen waje, dake halartar taron Asiya na Boao na bana, da ya jagoranta a yau Alhamis, Li Qiang ya jaddada cewa, gwamnatin Sin na fatan yin aiki tare da ’yan kasuwa, ta yadda za su karfafa kansu a wannan lokaci da duniya ke fuskantar yanayi na rashin tabbas, kana su karfafa kwarin gwiwar su, da daidaita burin da suka sanya gaba, su ci gaba da ingiza matakan ingantawa, da bunkasa ci gaba a kasar Sin, da Asiya da duniya baki daya.
Yayin zaman, wakilan ’yan kasuwa daga Japan, da Sin, da Amurka, da Korea ta Kudu, da Birtaniya, da Italiya da sauran kasashe sun gabatar da jawabai, wadanda suka bayyana aniyar manyan kamfanonin kasa da kasa, na ci gaba da zuba jari a kasar Sin, da wanzar da ci gaba na tsawon lokaci a kasar. (Faiza Mustapha, Saminu Alhassan)