Firaministan kasar Sin Li Qiang ya gana da takwaransa na kasar Cote d’Ivoire Patrick Achi wanda ya halarci taron dandalin tattaunawar Asiya na Boao na shekarar 2023 a lardin Hainan na kasar Sin a yau.
A yayin ganawar, Li Qiang ya yi nuni da cewa, Sin ta yabawa kasar Cote d’Ivoire domin ta goyi bayan shawarar “ziri daya da hanya daya”, da kiran samun bunkasuwar duniya, da kiran kiyaye tsaron duniya, da tsayawa tsayin daka kan manufar Sin daya tak a duniya. Kana kasar Sin za ta ci gaba da goyon bayan kasar Cote d’Ivoire da ta bi hanyar zamanintar da kasa dake dacewa da yanayinta, da mai da hankali ga hadin gwiwa dake tsakanin bangarorin biyu a fannoni daban daban.
A nasa bangare, Patrick Achi ya godewa kasar Sin bisa gudummawar da ta samar wa Cote d’Ivoire wajen yaki da cutar COVID-19 da raya ayyukan more rayuwa. Ya ce kasar Cote d’Ivoire ta tsaya tsayin daka kan ka’idar Sin daya tak a duniya, da shiga hadin gwiwar dake tsakanin kasashe masu bin shawarar “ziri daya da hanya daya”, kana kasarsa tana son amfani da damar cika shekaru 40 da kulla dangantakar diplomasiyya tsakaninta da kasar Sin, wajen kara zuba jari da hadin gwiwa a fannonin aikin noma, da ba da ilmi, da harkokin matasa da sauransu, don taimakawa kasar Cote d’Ivoire wajen gaggauta bunkasa tattalin arziki da zamantakewar al’umma da kuma masana’antu. (Zainab)