Da safiyar yau Laraba, firaministan kasar Sin Li Qiang ya gana da shugaban kasar Najeriya Bola Tinubu, wanda ke halartar taron kolin dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afirka wato FOCAC da ma ziyarar aiki a nan kasar Sin.
Li ya ce, shugaba Xi Jinping ya gana da malam shugaban jiya, sun sanar da daga huldarsu zuwa dangantakar abota bisa manyan tsare-tsare daga dukkan fannoni. A matakin farko, Sin na fatan zurfafa amincewa ta fuskar siyasa da habaka hadin gwiwarsu da taimakawa juna a kan hanyar samun bunkasuwa cikin hadin kai, bisa manyan tsare-tsare karkashin jagorancin shugabannin biyu.
A nasa bangare, shugaba Bola Tinubu ya ce, huldar abota bisa manyan tsare-tsare daga dukkan fannoni tsakanin kasashen biyu ya ginu bisa tushen daidaito da samun moriyar juna. Najeriya na fatan inganta tuntubar juna a fannin cinikayya da zuba jari da manyan ababen more rayuwa da sana’ar samar da kayayyaki da ba da ilmi da al’adu da sauransu karkashin tsarin FOCAC, ta yadda za su ingiza huldarsu zuwa gaba bisa sabon mafari. Najeriya na maraba da karin kamfanonin Sin da su zuba jari a kasar. Yana mai alkawarin samar musu yanayin tsaro mai kyau. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp