A jiya 30 ga watan Satumba, firaministan kasar Sin Li Qiang ya mika sakon taya murna ga Safi Kharib bisa zama sabon firaministan kasar Algeria.
Li Qiang ya bayyana cewa, Sin da Algeria sun sada zumunta mai zurfi da juna. A cikin shekaru 67 da kulla dangantakar diflomasiyya a tsakanin kasashen biyu, an raya dangantakarsu yadda ya kamata, da yin kokari tare da nuna goyon baya ga juna. A watan Yuli na shekarar 2023, shugaban kasar Algeria Abdelmadjid Tebboune ya kai ziyara a kasar Sin cikin nasara, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi shawarwari tare da shugaba Tebboune, batun da ya samar da taswirar raya dangantakar kasashen biyu bisa manyan tsare-tsare.
Sin ta maida hankali sosai kan raya dangantakar dake tsakaninta da kasar Algeria, firaminista Li Qiang yana son yin kokari tare da firaminista Kharib wajen aiwatar da ayyukan da kasashen biyu suka cimma daidaito, da yin imani da juna, da zurfafa hadin gwiwa, don sa kaimi ga raya dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni a tsakanin kasashen biyu zuwa sabon matsayi. (Zainab Zhang)