Firaministan kasar Sin Li Qiang, zai halarci taro karo na 24 na majalisar shugabannin gwamnatocin kasashe membobin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai ko SCO, wanda zai gudana a ranakun 17 da 18 ga watan Nuwamban nan a birnin Moscow na kasar Rasha, bisa gayyatar da firaministan kasar Mikhail Mishustin ya yi masa.
Wata sanarwar da ta fito daga ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin a yau Alhamis, ta ce Li Qiang zai kuma gudanar da ziyarar aiki a kasar Zambia a ranakun 19 da 20 ga watan nan, bisa gayyatar da gwamnatin Zambia ta yi masa.
Kazalika, firaministan na Sin zai halarci taron kungiyar G20 karo na 20 a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta Kudu, tsakanin ranakun 21 zuwa 23 ga watan nan, bisa gayyatar gwamnatin Afirka ta Kudu. (Saminu Alhassan)














