Wani likita dan Nijeriya, Julius Oni wanda kwararren farfesa ne a fannin tiyata ya bayyana cewa, ya bar aikinsa ne a asibitin Johns Hopkins da ke Amurka saboda hukuncin da ya yanke na kashin kansa na komowa Nijeriya bayan ya shafe shekaru 25 yana zaune a kasar.
Oni ya bayyana hakan ne a shafinsa na Tiktok, inda ya bayyana cewa, ya dauki hutu na makonni shida a wurin aiki kafin ya dawo, wanda hakan ke nuna cewa, da ra’ayin kansa ya komo Nijeriya.
- Sin Ta Kira Taron Nazarin Yanayi Da Aikin Raya Tattalin Arzikin Kasar
- Sake Dawo Da Sanusi II Sarautar Kano Ya Fi Min Komai Dadi – El-Rufai
Oni ya bayyana cewa, ya sayar da kadarorinsa da suka hada da gida da motoci, sannan ya dawo Nijeriya tare da matarsa da ‘ya’yansa.
Ya kuma bayyana kudurinsa na bai wa majinyatan Nijeriya kulawar kiwon lafiya mafi inganci kamar na Amurka.