Ministan lafiya da walwalar al’umma, Farfesa Muhammad Ali Pate, ya nuna damuwarsa kan yadda likitocin Nijeriya suke sulalewa su na fita zuwa kasashen waje.
Ya misalta da cewa abun damuwa inda likitoci masu lasisi guda dubu 55,000 kacal ne ke kula da lafiyar illahirin al’umman da suka zarce miliyan 200.
Ministan wanda ke magana a hirarsa da wata gidan talabijin, ya ce sama da likitoci 16,000 ne suka sanya kafa suka fice daga Nijeriya a cikin shekaru biyar da suka gabata, yayin da wasu kari su 17,000 aka musu sauyin wajen aiki.
Farfesa Pate ya lura kan cewa ficewar likitoci, jami’an kiwon lafiya da sauran kwararru a wasu fannoni domin zuwa kasashen waje amsar ayyuka masu gwabi, yayin da kasar nan kuma take dan amfani da sauran wadanda suka rage.
A cewarsa, Nijeriya tana da sama da kwararru a bangaren kiwon lafiya sama da 300,000 da suka hada da likitoci, nas-nas, unguzoma, kwararru a bangaren harhada maguna, masu gwaje-gwajen kimiyya da sauransu.
Ya ce, “Mun gudanar da bincike inda muka gano cewa muna da likitoci masu rajista a Nijeriya guda 85,000 zuwa 90,000. Sai dai ba dukkaninsu ke cikin kasar ba.
“Wasu daga cikinsu sun tafi kasashen ketare, musamman Amurka da Burtaniya. Amma, muna da likitoci masu rajista 55,000 a kasar nan.”
Ya ce hatta wasu ‘yan matsaloli da ake samu a bangaren kiwon lafiya na da nasaba da rashin wadatattun jami’an kiwon lafiyar ne, inda ya nuna matukar damuwarsa kan hakan.
A cewarsa, ba daidai ba ne Nijeriya ta ci gaba da rasa hazikan ma’aikatanta, musamman likitoci ga kasashen waje, ya nuna cewa an fi tsananin bukatar su a nan gida Nijeriya.