Kongo (Brazzaville), tana yamma maso tsakiyar nahiyar Afirka. A yammacin Brazzaville, babban birnin kasar, akwai asibitin sada zumunta na kasar Sin da Congo, wanda aka gina shi da taimakon kasar Sin, wanda kuma cikin shekaru 10 da suka gabata, a kai a kai ya zama asibiti mafi samun karbuwa a kasar Kongo.
A Kongo (Brazzaville) dake cikin yankin equatorial, abu ne mai sauki mutane su kamu da cututtukan ido, amma likitocin wurin dake iya yin tiyatar ido ’yan kadan ne. Tare da goyon bayan “Aikin tallafi tsakanin asibitoci” na kasar Sin, asibitin sada zumunta na Sin da Kongo ya kafa cibiyar kula da ido ta kasar Sin da Kongo (Brazzaville), wanda cikin sauri ya zama sashen da ya fi karbar adadin masu fama da ciwo a asibitin.
- CMG Ya Hada Gwiwa Da Kafofin Yada Labaru Na Kasashen Da Ke Bin Shawarar “Ziri Daya Da Hanya Daya”
- Xi Ya Fadawa Schumer Yadda Sin Da Amurka Za Su Daidaita Zai Tabbatar Da Makomar Bil Adama
A ranar 30 ga watan Maris na shekarar 2013, lokacin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ziyarci kasar Congo (Brazzaville), ya ziyarci tawagar likitocin kasar dake gudanar da ayyukan ba da agaji a asibitin sada zumunta na Sin da Kongo, inda a karo na farko ya gabatar da ruhin tawagogin likitocin kasar Sin, wato “Ba tsoron wahala, kokarin ba da gudummawa, ceton rayuka da warkar da wadanda suka ji rauni, da nuna kauna marar iyaka”.
Shekaru 10 ke nan, a watan Fabrairun shekarar 2023, shugaba Xi Jinping ya sake ambaton ruhin tawagar likitocin kasar Sin, yayin da yake ba da amsa ga rukuni na 19, na tawagar likitocin kasar Sin dake ba da agaji a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.
A cikin shekaru 10 da suka gabata, kasar Sin ta aike da tawagar likitoci fiye da 6,000 zuwa kasashe 58, wadanda suka yi wa mutane miliyan 22 hidima a kasashen da suka samu tallafin, kana ta gudanar da ayyukan ba da jinya ba tare da karbar kudi ba har kusan dubu daya. (Mai fassara: Bilkisu Xin)