Likitocin kasar Sin dake aiki a Saliyo, sun gabatar da bita ta musamman game da matakan kandagarki, da magance cutar zazzabin cizon sauro ko malaria ga likitocin kasar.
Yayin bitar ta jiya Alhamis, wadda aka gudanar a asibitin sada zumunta na Sin da Saliyo, jagoran tawagar likitocin na Sin Zhan Xinjie, wanda kwararre ne a fannin gwaje gwajen cututtuka, ya gabatar da makala game da cutar ta Malaria, da nau’o’in sauro dake baza ta a sassan duniya daban daban, inda kuma ya yi fashin baki game da dabarun gano cutar da ake amfani da su a dakunan binciken kwayoyin cuta.
A cewar Zhan Xinjie, burinsu shi ne zurfafa fahimta game da cutar, tare da aiki kafada da kafada, wajen inganta ayyukan kandagarki da magance cutar ta hanyar samar da horo.
A nasa bangare kuwa, daya daga likitocin Saliyo dake aiki a asibitin Sallieu Kamara, godewa likitocin kasar Sin ya yi bisa yadda suka tsara cikakken horo ga takwarorinsu na Saliyo. Yana mai cewa, ilimin da suka koya zai taimaka musu wajen gaggauta gano cutar ta malaria.
Kamara ya ce har yanzu, asibitin nasu na da karancin kayayyakin aiki na binciken cutar, don haka ya gabatar da roko ga bangaren na Sin, da ya ci gaba da tallafawa.
Ya ce “Kwarewa da muke samu ta hanyar horas da jami’an lafiya, na taka rawar gani wajen kubutar da rayukan karin al’ummar mu”. (Saminu Alhassan)