Tawaga ta 25 ta likitocin kasar Sin dake aiki a kasar Saliyo, da hadin gwiwar wasu kwararru daga cibiyar kandagarki da shawo kan cututtuka ta kasar Sin, sun taimakawa al’ummun Saliyo da dabarun magance cutar zazzabin cizon sauro ko Malaria.
Likitocin na kasar Sin sun kaddamar da shirin samar da hidimomin kiwon lafiya na yini biyu kyauta tun daga ranar Laraba ga al’ummar Rogbangba, a wani bangare na bikin ranar Malaria ta kasa da kasa wadda a bana ta fado ranar 25 ga watan Afrilun nan.
- Wang Yi: Amurka Ba Ta Da Alfarma Ko Gatan Kin Biyayya Ga Dokokin Kasa Da Kasa
- Baje Kolin Kayayyakin Amfani Na Kasa Da Kasa Na Sin Ya Gabatar Da Fitattun Kamfanoni Sama Da 4019
Da yake tsokaci kan gudummawar likitocin, shugaban tawagar jami’an lafiyar na kasar Sin Lu Chaoqun, ya ce cutar malaria babbar barazana ce ga rayukan al’ummun Saliyo, kuma shirin da suka kaddamar na da burin samar da kandagarki ga yaduwar cutar, da inganta tsafta tsakanin al’ummun yankin.
Ita ma babbar jami’ar shirin yaki da cutar zazzabin cizon sauro a Saliyo Anita Kamara, ta ce dukkanin al’ummar Saliyo na da hakkin samun hidima mai nagarta, mai rahusa kuma kan lokaci, ta ganowa, da magance cutar Malaria, duk da cewa har yanzu hakan ba ta kai ga samuwa ba.
A nasa bangare kuwa, limanin majami’ar al’ummar Rogbangba James Clifford, jinjinawa likitocin ya yi bisa yadda har kullum suke tunawa da al’ummar yankin, wanda hakan a cewarsa wata ni’ima ce. (Saminu Alhassan)