Tawagar likitocin da gwamnatin kasar Sin ta tura birnin Yaounde, fadar mulkin kasar Kamaru a karo na 22, ta gudanar da jinyar marasa lafiya kyauta, tsakanin ranekun 20 zuwa ta 22 ga wannan wata, aikin da ya samu matukar karbuwa tsakanin al’ummun birnin.
An gudanar da ayyukan jinyar kyauta ne a babban ginin gwamnatin birnin, inda likitocin kasar Sin 8 suka samar da hidimar kula da marasa lafiya sama da 650, tare kuma da ba da tallafin magunguna, da sauran kayayyakin kiwon lafiya.
Tun daga shekarar 1975, gwamnatin kasar Sin ta tura jimillar tawagogin likitoci 22 zuwa kasar Kamaru, kuma adadin likitocin na Sin da suka yi aiki karkashin tawagogin ya kai 736, inda suka yi jinyar marasa lafiya dake fama da cututtuka a wuraren daban daban a fadin kasar. (Mai fassarawa: Jamila)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp