A wani ci gaba mai cike da ban al’ajabi a fannin likitanci, tawagar wasu likitocin Saudiyya masu aikin tiyata a karkashin jagorancin yariman Saudiya mai jiran gado, Mohammed bin Salman bin Abdulaziz, sun kammala aikin tiyatar raba wasu tagwayen ‘yan Nijeriya biyu, Hassana da Husaina, a asibitin kwararru na Sarki Abdullah da ke birnin Riyadh.
Tagwayen wanda aka haifa a Nijeriya, sun isa birnin Riyadh a ranar 31 ga Oktoba, 2023, inda aka gudanar da gwaje-gwaje na musamman da ke wuraren da za a bi yayin gudanar da aikin don raba su, wanda ya hada da duba ƙashin ƙugu da ƙananan kashin baya da ƙananan jijiyoyi.
- Tagwayen Da Aka Haifa Manne A Kano Sun Tashi Zuwa Saudiyya Domin Raba Su
- Hajjin 2023: Alhazan Nijeriya 14 Sun Rasu A Saudiyya A Aikin Hajin Bana
Wannan aikin tiyatar shi ne aiki karo na 60 da wani shirin lafiya a Saudiyya ta yi na raba tagwaye, shirin ya samar da kula da yin aiki ga tagwaye 135 daga kasashe 25 a cikin shekaru 34 da suka gabata.
Dr. Al Rabeeah ya mika godiya ga mahukuntan Saudiyya bisa goyon bayan da suke ba wa shirin da kuma nasarar raba ‘yan biyun Nijeriya, sannan ya kara nuna jin dadinsa kan yadda harkar lafiyar kasar Saudiyya ta bunkasa.