Daraktan sashen kula da huldar kasashen waje na JKS, Liu Jianchao ya gana a jiya Juma’a da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken a birnin Washington. Bangarorin biyu sun bayyana fatansu na ci gaba da shawarwari da hadin kai, da ingiza tabbatar da matsaya daya da nasarorin da shugabannin kasashen biyu suka cimma a ganawar San Francisco. Liu Jianchao ya kuma bayyana matsayin Sin kan wasu batutuwa, inda ya nanata cewa, kamata ya yi bangarorin biyu sun hada kai da bin hanya iri daya, ta yadda za su ciyar da huldarsu gaba da ganin dorewarta cikin lokaci mai tsawo. Ban da wannan kuma, sun yi musanyar ra’ayi game da batutuwan duniya da na shiyya-shiyya. (Amina Xu)