Shugaban sashin tuntubar kasashen waje na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, Liu Jianchao, ya jagoranci tawagar jam’iyyar kwaminis zuwa kasar Rasha a jiya Jumma’a 16 ga watan nan, don halartar babban taron kafa dandalin tattaunawa tsakanin jam’iyyun siyasar kasa da kasa, mai taken “yaki da sabon ra’ayin mulkin mallaka”, tare da gabatar da jawabi.
Jami’in ya ce, har yanzu ana samun bullar nau’o’in mulkin mallaka a duk fadin duniya, abun dake haifar da illa sosai ga duniya. Don haka ya yi kira ga sassan kasa da kasa da su kare hakkokinsu na samar da ci gaba, da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya, da taimakawa ga cudanyar mabambantan wayewar kai, da kawo sauyi ga tsarin tafiyar da harkokin duniya, tare da gina al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya.
A yayin taron, jami’in ya kuma gana da shugaban jam’iyyar United Russia, Dmitry Medvedev. (Murtala Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp