• English
  • Business News
Thursday, May 15, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Liu Xiabing: Matashiyar Da Ke Kokarin Raya Sana’ar Gargajiya Ta Yin Saka Da Gora

by CMG Hausa
2 years ago
in Daga Kasar Sin
0
Liu Xiabing: Matashiyar Da Ke Kokarin Raya Sana’ar Gargajiya Ta Yin Saka Da Gora

Liu Xiabing wadda ke kwarewar saka kaya da gora

Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Liu Xiabing, mai shekaru 31 da haihuwa, ’yar asalin garin Pingnan na gundumar Lingshan ta larin Guangxi dake kudu maso yammacin kasar Sin ce. Kayayyakin da ake sakawa da gora na Lingshan sanannu ne, kuma ana sayar da su a kasashen waje, kuma a da sun taba kasancewa tushen samun kudin shiga na mazauna wurin.

Bayan rikicin hada-hadar kudi da ya barke a shekarar 2008, sana’ar saka da ake amfani da gora ta Lingshan, ita ma ta soma komawa baya sannu a hankali. Amma, Liu Xiabing ba ta taba yin la’akari da yin watsi da sana’ar ba. Tana kallon yadda gyalen gora ke juyawa a karkashin yatsan kakanninta, kuma ba a dauki lokaci mai tsawo ba suka zama kwanduna ko kwandunan kura. Ta tuna cewa mahaifinta ya fara aikinsa a matsayin mai sana’a da hannu daga sakar hular gora. Daga baya, bayan da iyalin suka fara sana’ar sakar ta amfani da gora, kayayyakin cinikayyar da suka kera da sayar su ne kayayyakin da ake bukata a zaman rayuwar yau da kullum.

  • Sin: Ya Kamata A Rika Girmama Akidun Mabiya Addinin Musulunci

Mahaifinsa ya ce, sana’ar ta yi kama da yadda rana ke faduwa, wato ba ta da kyakkyawar makoma. Amma Liu Xiabing ba ta yarda da haka ba, har ma ta yi ta kokarin farfado da sana’ar. Ta yi fama da rashin nasara da yawa, kuma a yayin da take cikin yanayi mafi muni, bashin da ta ci, ya kai kusan dalar Amurka dubu 300. Wata rana, lokacin da take sayar da kayayyaki kai tsaye ta yanar gizo, maganganun da masu kallo suka yi sun sanya ta samu wata hanyar farfado da sana’arta ta sakar da ake amfani da gora. Ta yi tunanin cewa, idan mutane ba sa bukatar wata hular da aka saka da gora, watakila za su bukaci wani gidan kyanwa da aka saka da gora.

Bayan ta gaza raya sana’arta har sau da dama, a karshe dai ta kaddamar da wani kayan cinikayya mai samun karbuwa kwarai da gaske wato gidan kyanwa, kuma ana iya sayar da irin wannan gidan kyanwa kusan dari biyu a kowace rana, inda ta samu jerin oda masu yawa har bayan tsawon watanni biyu.

Daga baya kuma, Liu Xiabing ta soma tsara wasu kayayyakin da suka shafi batun kyanwa, ban da gidan kyanwa, akwai su jakar ajiye kyanwa, kayan wasan na kyanwa da dai sauransu. A cewarta, “Ban san inda bukatun jama’a za su biyo baya ba, amma ina so in kama wannan damar in nemi wata hanyar ci gaba, ga wannan sana’ar gargajiya ta saka da ake amfani da gora.”

Labarai Masu Nasaba

Bude Kasar Sin Na Kyautata Ci Gaban Duniya

Mu Leka Jihar Mongolia Ta Gida Dake Arewacin Kasar Sin

Liu Xiabing
Liu Xiabing na sayar da kayan gora da ta saka ta yanar gizo

Tun da Liu Xiabing ke karama, ta iya gano nau’ikan kayan sakar da aka yi amfani da gora a ko’ina a cikin gidan su, kamar su kwandunan ’ya’yan itace, kwandunan abinci, kwandunan kura… Abin da ya fi zama ruwan dare a gidan shi ne hular gora, wanda shi ne abu na farko da mahaifinta ya koya, bayan ya soma shiga masana’antar saka. Abubuwan da aka saka da gora suna da juriya, da dorewa, kuma ba su da tsada, hakan ya sa su kasance kayan gida da suka fi samu karbuwa a wancan lokacin.

A garin Pingnan, kusan kowane iyali ya san yadda ake saka da gora, wanda kuma ya kasance aiki ga yawancin mutane don ciyar da iyalansu.
Karkashin gado, da inganta sana’ar saka da masu sana’a zuriya daga zuriya suke yi, yanzu kayayyakin saka da gora na Lingshan ya shahara sosai a duniya. Masu saye suna ta shiga garin Pingnan, kuma suna sayar da kayayyakin da aka saka da gora zuwa duk fadin kasar Sin da ma kasashen waje. Liu Xiabing ta tuna da cewa, a lokacin kuruciyarta, danginta sun tsunduma cikin harkokin kasuwancin waje, na sayar da kayan saka da ake amfani da gora, saboda haka, iyalinta na rayuwa sosai kuma ba sa bukatar damuwa game da kudi.

Amma, komai ya sauya bayan barkewar rikicin kudi a shekarar 2008. Odar ciniki daga kasashen waje ta bace sannu a hankali, tsoffin abokan cinikayyarsu ko dai sun canza ayyuka, ko kuma sun fita daga kasuwanci, haka ma iyalin Liu Xiabing sun ya yi asarar kashi 80% na hanyoyin samun kudin shiga. Sakamakon haka, matsayin zaman rayuwarsu ya ragu sosai, mahaifinta na gajiyawa a ko wace rana. Da ganin haka, sai Liu Xiabing ta gabatar da bukatarta ta koyon fasahar saka, amma mahaifin ta ya ki bukatar a kai a kai. Saboda a ganinsa, aikin nan na wahala ne kwarai, baya ga haka kuma, sana’ar ba ta da makoma mai kyau.

Liu Xiabing
Liu Xiabing da iyayenta

Tun daga wannan shekarar, sana’ar saka da ake amfani da gora a garin Pingnan ta soma ja da baya sannu a hankali, ya zuwa shekarar 2015, babu masu sana’ar da yawa a garin. Wasu mutane suna aiki a waje, wasu kuma suna aikin noma a gida. Yayin da dazuzzukan gora a cikin tsaunuka ke girma sosai, sana’ar saka dake amfani da gora a Lingshan na raguwa sannu a hankali, kuma mutane kadan ne suka damu da hakan.

Liu Xiabing ta kasance tana kiyaye masana’antar saka dake amfani da gora a ko da yaushe. Bayan ta kammala karatu, daga shekarar 2009 zuwa ta 2015, a cikin shekarun bakwai, ta yi kokari sau da yawa don komawa garin Pingnan, don farfado da fasahar saka dake amfani da gora, amma sau da yawa ta kasa.

A shekara ta 2016, ta sake komawa garinsu, kuma ta fara kokarin yin amfani da yanar gizo don sake gina kasuwancin iyalinta na gudanar da cinikayyar waje. A wannan karo, abokan ciniki sun fara dawowa sannu a hankali, kuma odar da ta samu sun karu a hankali. Sakamakon bukatun da ake da su, iyalin Liu ya zama jagora wajen farfadowar fasaha da sana’ar saka da ake amfani da gora ta Lingshan. Mahaifin Liu Xiabing, Liu Jiasheng, shi ma ya zama wakilin magajin gadon “Fasahar saka da ake amfani da gora ta Lingshan”.

Amma, ba cikin sauki ba ta gudanar da wannan aikin, saboda ta dauki matakai da yawa wadanda ba su dace da halin da take ciki ba, don bude kantin sayar da kaya ta yanar gizo, don haka, ta sake yin kasa, har ma bashin da ta ci ya kai kusan dalar Amurka dubu 300.

Liu Xiabing
Gidajen kyanwa da Liu Xiabing ta saka da gora

Wata rana a cikin watan Maris na shekarar 2021, Liu Xiabing tana gabatar da samfuranta a dakin watsa shirye-shirye kai tsaye na yanar gizo. Ba zato ba tsamani, mutane da yawa sun shiga dakin watsa shirye-shiryen kai tsaye, duk suna cewa, “Sai ki yi gidan kyanwa da gora”. A yawancin lokaci, babu mutane da yawa a dakin ta, in ban da kimanin mutane sama da 20 kadan, don haka, da ganin yawan mutane kamar haka, da kuma maganarsu, Liu Xiabing ta rude sosai, ba ta san me ke faruwa ba.

Daga baya Liu Xiabing ta bi diddigin sharhin masu amfani da yanar gizo, inda a karshe ta gano dalilin. Wani ya ba da shawarar cewa, ya yi amfani da irin wannan babban kwandon ‘ya’yan itace a matsayin gidan kyanwa, wanda ya dace sosai, kuma ya dauki bidiyo game da haka a yanar gizo, wanda ya jawo hankulan masu kiwon kyanwa da yawa.

Liu Xiabing ta fahimci sosai cewa, wannan na iya zama wata dama mai kyau. Washe gari, ta je ta nemo mahaifinta, bayan tattaunawa sosai, suka tsara wani zane mai sauki game da gidan kyanwa, kuma suka ba wa wani mai saka, don ya yi samfurin, a duba ko zai iya samun karbuwa ko a’a.

A wannan rana da yamma, Liu Xiabing ta kwatanta samfurin, kuma ta yi saka a dakin watsa shirye-shiryen kai tsaye. Tana sakar gidan kyanwa a hankali, kuma masu amfani da yanar gizo suna hira da juna. Bayan sa’o’i sama da hudu, ta sayar da gidajen kyanwa kusan 200, adadin ya wuce yadda take tsammani.

Ga lokacin zuwa kwanaki 10 masu zuwa, ta sayar da gidajen kyanwa na gora yadda ya kamata, wadanda yawansu ya kai kusan 2000, inda ta samu jerin oda masu yawa har bayan tsawon watanni biyu.
Duk kayan da a saka da gora na bukatar matakai masu yawa.

Liu Xiabing
Zaman rayuwar mazauna garin Pingnan na samun kyautatuwa sakamakon sana’ar saka da gora

Da farko, akwai bukatar a tafi daji don yanko gora. Gora na da nauyin, mai karfi na iya daukar uku ko hudu a baya, ga gajere kamar yadda Liu Xiabing take, tana shan wahala wajen dauke guda daya kawai.
Liu Xiabing ta ce, kayan aiki daban-daban suna bukatar zabar gora irin daban-daban. Ga misalin, gidan kyanwa na bukatar kayan aiki masu karfi, don haka dole ne a zabi gora mai shekaru hudu ko biyar, game da wadancan abubuwa kamar kwandunan ‘ya’yan itace, gora mai shekaru uku ko hudu ne ake bukata shi ke nan.

Bayan an raba cikakken bututun gora, ana bukatar kara raba su zuwa sili daban-daban bisa kauri da fadi, ana gudanar da wadannan matakai masu wahala ne domin share fagen aikin saka da za a yi nan gaba. Alal misali, sakar wani kwandon ‘ya’yan itace na bukatar nau’ikan sili guda 6. Saka gidan kyanwa ya samo asali ne a kan sakar kwandunan ‘ya’yan itace, amma, bisa ga bukatun masu kiwon kyanwa, an kara karin mataki na samar da sauti.

Kowace rana, a cikin ma’ajin gidan Liu Xiabing, akwai wasu ‘yan’uwa mata dake zaune a kan kujera, suna saka wani gidan kyanwa akan cinyar su, hannayensu suna goge kan silin gora, hakan yana sa hannayen su kurjewa, sai dai daga baya su yanke wurin. Wani gidan kyanwa mai fadi santimita 40, yana bukatar kwararren ma’aikaci ya yi awa uku ko hudu don kammalawa, idan aka kara lokacin shiryawa, to za a yi amfani da awa kusan biyar domin kammala dukkan aikin.

Bayan an farfado da sakar dake amfani da gora ta Lingshan, masu saka da yawa sun koma garinsu na Pingnan, sun kama wannan tsohuwar sana’a ta gargajiya. Suna son irin wannan aiki, saboda ba za su bar gida ba, suna iya samun kudin shiga a yayin da suke kulawa da tsoffi da yara. Sannu a hankali, zaman rayuwar mazauna kauyen na samun kyautatuwa. Ya zuwa yanzu, iyalin Liu Xiabing ya jagoranci masu saka sama da 600 su kara samun kudin shiga ta hanyar sayar da kayan da ake saka da gora, matasa da yawa ma sun soma koyon wannan fasahar gargajiya.

Kullum Liu Xiabing na ganin cewa, sana’ar saka da gora, wata sana’a ce mai fa’ida. Bayan gidan kyanwa da aka saka da gora ya samu karbuwa, sai ta ji cewa tana da sabon tunani kan makomar sana’arta a nan gaba.
Baya ga ci gaba da sayar da kayayyakin cinikayya na gargajiya da aka saka da gora, kuma tana tsayawa kan gidan kyanwa, don fitar da jerin wasu sabbin dabaru daya bayan daya game da kayan dabbobi. Ta tsara jakar kyanwa mai gida gida, da gidan kyanwa, da kuma wasu kayayyakin wasan kyanwa, wasu ma ta tsara ne bisa shawarar masu kallo yanar gizo.

Sana’ar saka da gora da kowane gida a garin Pingnan ke iya yi tana nuna wani sabon yanayi sakamakon saurin ci gaban yanar gizo, da kokarin matasan da suka dawo gida don fara sana’o’insu.
Bayan rana ta fadi, ko shakka babu za ta sake fitowa…


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Yunkurin Japan Na Janyo NATO Cikin Yankin Asiya Da Fasifik Ba Zai Haifar Da Da Mai Ido Ba

Next Post

A Babban Taron Kamfanin LEADERSHIP Karo Na 14…An Zakulo Abubuwan Da Za Su Kawo Nasara Ko Cikas Ga Zaben 2023

Related

Bude Kasar Sin Na Kyautata Ci Gaban Duniya
Daga Kasar Sin

Bude Kasar Sin Na Kyautata Ci Gaban Duniya

3 months ago
Mu Leka Jihar Mongolia Ta Gida Dake Arewacin Kasar Sin
Daga Kasar Sin

Mu Leka Jihar Mongolia Ta Gida Dake Arewacin Kasar Sin

10 months ago
wang lili
Daga Kasar Sin

Yadda Wang Lili Ke Kiyaye Neman Cimma Nasara A Wasan Kwallon Kwando

10 months ago
Kumbon Sin Ya Tashi Daga Bangaren Duniyar Wata Mai Nisa Dauke Samfura
Daga Kasar Sin

Kumbon Sin Ya Tashi Daga Bangaren Duniyar Wata Mai Nisa Dauke Samfura

11 months ago
Zambiya
Daga Kasar Sin

’Yar Kasar Zambiya: A Nan Kasar Sin, Ina Jin Tamkar Ina Gida!

1 year ago
Ba Shakka Kamfanonin Ketare Za Su Ci Riba In Suka Zuba Jari Da Aiwatar Da Ayyukansu A Sin
Daga Kasar Sin

Ba Shakka Kamfanonin Ketare Za Su Ci Riba In Suka Zuba Jari Da Aiwatar Da Ayyukansu A Sin

1 year ago
Next Post
A Babban Taron Kamfanin LEADERSHIP Karo Na 14…An Zakulo Abubuwan Da Za Su Kawo Nasara Ko Cikas Ga Zaben 2023

A Babban Taron Kamfanin LEADERSHIP Karo Na 14...An Zakulo Abubuwan Da Za Su Kawo Nasara Ko Cikas Ga Zaben 2023

LABARAI MASU NASABA

‘Yansanda Sun Musanta Zargin Kai Wa ‘Yan Bindiga Abinci Ta Jirgin Sama A Kogi

‘Yansanda Sun Musanta Zargin Kai Wa ‘Yan Bindiga Abinci Ta Jirgin Sama A Kogi

May 15, 2025
Gabar ‘Yan Bindiga A Tsakaninsu Ta Kara Tsanani A Zamfara

’Yan Bindiga Sun Sace Mutane 200 A Mazaɓa Ta A Zamfara – Ɗan Majalisar Tarayya

May 15, 2025
An Yi Wa ‘Yar Shekara 18 Fyade Har Lahira A Taraba

’Yansanda Sun Cafke Mutane 9 Kan Kisan Jigon Jam’iyyar PDP A Adamawa

May 15, 2025
UTME

ASUU Ta Yi Barazanar Maka JAMB A Kotu Biyo Bayan Samun Mummunan Sakamako A UTME

May 14, 2025
Xi Jinping Ya Gana Da Takwarorinsa Na Kasashen Colombia Da Chile

Xi Jinping Ya Gana Da Takwarorinsa Na Kasashen Colombia Da Chile

May 14, 2025
Gwamnatin Tarayya Da Majalisar Dokoki Za Su Haɗa  Gwiwa Kan Sake Duba Dokar Laifukan Intanet — Minista

Gwamnatin Tarayya Da Majalisar Dokoki Za Su Haɗa  Gwiwa Kan Sake Duba Dokar Laifukan Intanet — Minista

May 14, 2025
Yadda Kasar Sin Ke Kokarin Gina Tashar Bincike A Sama Da Tubalin Kasar Duniyar Wata

Yadda Kasar Sin Ke Kokarin Gina Tashar Bincike A Sama Da Tubalin Kasar Duniyar Wata

May 14, 2025
gaza

Kasafin Kudi Na Naira Tiriliyan 1.78 Na Abuja Ya Tsallake Karatu Na Biyu A Majalisa

May 14, 2025
Kasar Sin Za Ta Inganta Cikakken Tsarin Fitar Da Ma’adanai Zuwa Ketare Don Kiyaye Tsaron Kasa

Kasar Sin Za Ta Inganta Cikakken Tsarin Fitar Da Ma’adanai Zuwa Ketare Don Kiyaye Tsaron Kasa

May 14, 2025
Tinubu Ya Yaba Wa Sule Lamiɗo A Taron Ƙaddamar Da Littafin Tarihin Rayuwasa

Tinubu Ya Yaba Wa Sule Lamiɗo A Taron Ƙaddamar Da Littafin Tarihin Rayuwasa

May 14, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.