A ranar 9 ga watan Afrilu, wakilin musamman na gwamnatin kasar Sin kan harkokin Afirka, Liu Yuxi, ya halarci bikin bude taron tattaunawa kan wayewar kan Sin da Afirka karo na uku a nan birnin Beijing, inda ya gabatar da jawabi.
Liu Yuxi ya bayyana cewa, yana fatan masana daga kasashen Afirka da Sin za su dauki taron tattaunawa kan wayewar kan Sin da Afirka na bana a matsayin wata dama ta kara habaka da fadada fahimtar juna, da kuma ba da karin goyon baya ta ilimi da tunani don zurfafa hadin gwiwar abokantakar Sin da Afirka a wannan sabon zamani, da gina babbar al’ummar Sinawa da Afirka mai makomar bai daya.
Taron tattaunawa kan wayewar kai na Sin da Afirka, wanda cibiyar nazarin harkokin Afirka ta kasar Sin ta shirya, wani muhimmin dandali ne na inganta mu’amalar al’adu tsakanin Sin da Afirka, da sa kaimi ga fahimtar wayewar kan al’ummomin Sin da Afirka. (Mai fassara: Yahaya)